✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta nemi amincewar Majalisa don karbo bashin $1.2bn daga Brazil

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta shigar da bukatar neman sahalewar Majalisar Dokokin Tarayya don karbo bashin dala biliyan 1.2 daga kasar Brazil domin daukar nauyin shirye-shirye…

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta shigar da bukatar neman sahalewar Majalisar Dokokin Tarayya don karbo bashin dala biliyan 1.2 daga kasar Brazil domin daukar nauyin shirye-shirye ayyukan noma da aka tsara a cikin kasafin kudin badi.

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Ahmed ce ta sanar da hakan yayin da ta bayyana a gaban Kwamitin Harkokin Kudi na Majalisar Wakilai a ranar Talata domin kare kasafin kudin da ma’aikatarta ta gabatar da hujja a kan kudin da ma’aikatar za ta bukata a badi.

Ministar ta ce Gwamnatin Tarayya ta aike wa da Majalisar Tarayyar bukatar karbo bashin daga kasar Brazil domin inganta ayyukan noma a Najeriya.

Ta ce Gwamnatin Tarayya za ta mallaki hekta 100,000 ta gona duk jiha a Najeriya domin noma kayan abinci tare da gina hanyoyi a wannan wurare don samar wa manoma damar kai amfanin gona zuwa kasuwanni da rage asarar ta ke biyo bayan girbi.

A wata zanta wa da Ministan Noma na Najeriya, Alhaji Sabo Nanono ya yi da BBC, ya ce za a karbo bashin ne domin zamanantar da aikin noma tare da inganta shi a kananan hukumomi 632 na kasar.

Minista Nanono ya ce za a yi amfani da wannan kudi wajen sayo motocin noma da kayan gyaransu da gina wuraren ajiye kayan feshi da magungunan kwari da sauransu.