✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati za ta dauki mataki akan masu yada labaran karya — Lai Mohammed

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta gargadi masu yada labaran karya da kalaman batanci akan cewar hakan na iya jefa kasa a cikin wani mawuyacin hali. Ministan…

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta gargadi masu yada labaran karya da kalaman batanci akan cewar hakan na iya jefa kasa a cikin wani mawuyacin hali.

Ministan yada labarai da al’adu Lai Muhammed, ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce gwamnati zata dauki mataki mai tsauri akan masu wannan dabi’a, domin kuwa a cewarsa matsala ce da take barazana ga zaman lafiya da kuma dorewar dimukuradiyyar Najeriya.

Ya kara da cewa, babu wata gwamnati da zata zuba ido ta bari labaran karya da kalaman batanci su mamaye kafafen yada labarai, a don hakane gwmnatin tarayya ta dauki aniyar kawar da wannan mummunar dabi’a a kasa baki daya.

Ministan ya roki ’yan jarida da su taimakawa yunkurin gwamnati don ganin an kawar da dabi’ar ta yada labaran karya da kalaman batanci.