A zaman taron majalisar zartarwa FEC da aka gudanar a jiya Laraba, gwamnati ta amince da yin kwangilar da zai lakume kudi Naira biliyan 2.8 wajen gyaran rage cunkosan da ake samu a gidajen yarin Najeriya.
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ne ya jagoranci taron majalisar da aka yi a fadar shugaban kasar Abuja, taron da ya kai sa’o’i uku ana tattaunawa akan batutuwa da dama
Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami ya bayyanawa manema labarai cewa, rage cinkosan `yan gidajen zai inganta harkokin shari’a a Najeriya.