✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Borno ta sanar da ranar da za su yi azumi kan Boko Haram

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da ranar Litinin 24 ga watan Fabrairun 2020 a matsayin ranar da za a gudanar da…

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da ranar Litinin 24 ga watan Fabrairun 2020 a matsayin ranar da za a gudanar da azumi da addu’o’i domin neman sauki da samun nasara kan mayakan Boko Haram.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi na minti shida da ya yi wa jama’ar jihar a ranar Laraba.

Ya kara da cewa, ranar Litinin din ba wai ranar hutu bace domin za a je aiki.

A dai ‘yan kwanakin nan mayakan Boko Haram sun yi ta kai hare-hare a unguwannin jihar, na bayan nan shi ne wanda aka kai garin Karamar Hukumar Chibok ranar Talata, yayin da maharan suka kai hari ranar Lahadin da ta wuce a garin Auno duk a cikin jihar.