✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Inuwa Yahaya ba ta warwaso ba ce – Barambu

Wani dan siyasa da ke Jihar Gombe Alhaji Abubakar Usman Barambu, ya ce gwamnatin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, gwamnatin al’umma ce da ba za ta…

Wani dan siyasa da ke Jihar Gombe Alhaji Abubakar Usman Barambu, ya ce gwamnatin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, gwamnatin al’umma ce da ba za ta bari a yi warwaso da dukiyar talakawa ba kuma gwamnati ce da ta san abin da take yi.

Alhaji Abubakar Barambu wanda aka fi sani da Buba Barambu, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Gombe.

Alhaji Abubakar Usman Barambu,    wanda ya bayyana cewa zai nemi tsayawa takarar Shugaban Karamar Hukumar Akko da ke Jihar Gombe ya bai wa Gwamna Inuwa Yahaya shawarar cewa duk wanda aka zaba a matsayin shugaban karamar hukuma bai yi wa al’umma daidai ba, Gwamnan ya sa a cire shi don kada ya bata masa suna a matsayinsa na Gwamnan talakawa.

Ya ce zai mayar da hankali wajen  magance matsalolin da ke damun al’ummar karamar hukumar, iinda ya ce yana da niyyar fitowa takarar neman shugabancin karamar hukumar ce don ciyar da yankin gaba.

Ya ce ya san yadda harkar ilimi da ruwan sha suke a karamar hukumar, don haka zai hada kai da gwamnatin jihar don magance matsalalolinta. Ya ce bangaren wutar lantarki kuwa tun a lokacin gwamnatin Sanata Danjuma Goje, ya kai wutar lantarki yankin amma yanzu wasu turakun wutar da yawa sun zube don haka babu wutar lantarki a yankin.

Alhaji Usman Barambu, ya ce kishin ya yi aiki da Gwamnan ne ya kara masa himma da kwazon neman ganin ya zama shugaban karamar hukumar don yankinsa ya shaida ribar romon mulkin siyasa a lokacinsa.

Sai ya yi kira ga al’ummar karamar wadda ita ce karamar hukuma mafi girma a Jihar Gombe su ba Gwamnan hadin kai da goyon baya don bukansa jihar.