✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Jihar Bauchi ta bukaci mahajjata su yi wa kasa addu’a

Alhazai 1,985 ne za su yi aikin Hajjin bana daga Jihar Bauchi inda wadansu daga cikin maniyyatan suka isa  Madina bayan sun tashi daga filin…

Alhazai 1,985 ne za su yi aikin Hajjin bana daga Jihar Bauchi inda wadansu daga cikin maniyyatan suka isa  Madina bayan sun tashi daga filin jirgin sama na Sa Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi

Amirul Hajji na Jihar, kuma Mataimakin Gwamnan Jihar, Sanata Baba Tela ya ce kwamitin da aka dora wa alhakin samar wa maniyyatan jihar muhallai da sauran bukatu suna can kasar Saudiyya, suna kokarin komai ya gudana yadda ya kamata ba tare da matsala ba.

Sanata Baba Tela ya yi alkawarin cewa kwamitin Amirul Hajjin zai yi aiki tukuru domin samun nasarar aikin.

Lokacin da Gwamnan Jihar Sanata Bala Mohammed yake bankwana da maniyyatan jihar a Bauchi, ya ce sun samar da shirye-shirye domin tabbatar da jin dadi da walwalar alhazan jihar.

Gwamnan ya ce sun samar da masaukan alhazan a kusa da Masallacin Harami domin tabbatar da rage matsalolin zirga-zirga da kuma sawwaka musu yadda za su rika samun Sallah cikin jam’i.

Gwamna Mohammed ya kuma sanar da cewa za su ba kowane Alhaji tallafin Riyal 300 domin samar musu da saukin rayuwa a Kasa Mai tsarki baya ga ragin da aka yi musu. Sannan za a rika bai wa maniyyatan abinci sau uku a rana don tabbatar da jin dadi da walwalarsu.

Gwamnan ya jawo hankalinsu kan su guji shiga cikin harkokin da ba su dace ba domin gudanar da aikin Hajji karbabbe. Sai ya roke su da su yi addu’a ga kasa da gwamnatinsa domin samun lafiya da zama lafiya da kuma neman Allah Ya kawo hanyar da za su warware dukkan matsalolin da ke damun Jihar Bauchi.

Babban Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Bauchi, Alhaji Dallami Shall ya ce gudunmawar da Gwamna Bala Mohammed ke ba hukumar shi ne irinsa na farko a tarihin hukumar, sai ya  gode wa Gwamnan saboda kokarin da yake yi don kyautata wa alhazai.

Wadansu daga cikin alhazan da Aminiya ta zanta da su; Bappayo Muhammad daga Karamar Hukumar Alkaleri da Larai Musa sun nuna jin dadinsu, sannan suka yi alkawarin yin biyayya da kuma bin dokokin kasa da na Saudiyya domin samun nasarar yin aikin hajjinsu.