✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana fita a Kajuru

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita na tsawon sa’a 24 wanda zata fara aiki nan take a garin Kasuwar Magani da ke karamar…

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita na tsawon sa’a 24 wanda zata fara aiki nan take a garin Kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kajuru.

Mataimakin gwamnan jihar, Barnabas Yusuf Bala, ya bada umurnin da a aiwatar da dokar hana fitan yadda kamata. Sa’annan ya bukaci jama’a da su yi da’a wa dokar, kuma su goyi bayan kokarin da a ke na wanzar da zaman lafiya a garin.

An dauki wannan matakin ne bayan wani zama da majalisar tsaron jihar ta yi a yau Juma’a.

An kuma tura jami’an tsaro yankin don tabbatar da zaman lafiya.