Search
Subscribe
Gwamnatin Najeriya ta haramta kungiyar tsaron Amotekun

Amotekun

Gwamnatin Najeriya ta haramta kungiyar tsaron Amotekun

Gwamnatin Najeriya ta sanar da haramta kungiyar tsaro ta Amotekun, da aka kaddamar a wasu jihohin shiyyar Kudu.

Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da Mai taimaka wa Ministan a fannin yada labarai Dakta Umar Jibrilu Gwandu ya shaidawa manema labarai jiya Talata.

Sanarwa na cewa, samar da tsaro da makami hakki ne da ya rataya kan gwamnatin Tarayya.

Kamar yadda kundin tsarin mulkin 1999 ya tanadar kirkiro kungiyar tsaro laifi ne da ya sabawa doka, domin an yi tanadin jami’an tsaron soji da na ‘yan sanda da na ruwa da kuma sojin sama, wadanda su ne ke da alhakin tabbatar da tsaro a dukkanin sassan Najeriya.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin