✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnoni ne matsalar Najeriya – Musalla

Wani dan takarar kujerar majalisar dokoki a Jihar Filato, a mazabar Jos ta Arewa Maso Arewa karkashin UPP, Malam Majiburrahman S. Musalla ya bayyana cewa…

Wani dan takarar kujerar majalisar dokoki a Jihar Filato, a mazabar Jos ta Arewa Maso Arewa karkashin UPP, Malam Majiburrahman S. Musalla ya bayyana cewa gwamnoni ne matsalar Najeriya a halin yanzu.

Musalla, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya. Ya ce gaskiya gwamnonin Najeriya suna nuna son rai tare da yin karfa-karfa a harkokin siyasa da harkokin mulki tare da taka kowa a jihohinsu. Kuma sai wanda suke so yake samun mukamin siyasa ko mukaman wasu harkoki na cigaban jama’a.

“Sakamakon wannan karfa-karfa da gwamnoni suke yi ‘yan majalisun jihohi sun zama ‘yan amshin shatansu, sai abin da gwamnonin suke so  suke aiwatarwa. Kuma gwamnonin basa yin wasu ayyuka na cigaba a jihohin nasu”.

Matashin ya ce ya kamata matasa da sauran al’ummar kasar nan, su tashi tsaye don ganin an magance wannan matsala ta gwamnoni a Najeriya.