Da Dumi Dumi

Gyara  girarki a zamanance

Idan aka ce gyaran gira ana nufin yadda za a kula da gira. Ma’ana

yadda gashin gira zai kasance.  Kamar yadda muka sani wasu mutanen suna da gashin gira mai yawa wanda kuma yake a barbaje wasu kuma za ki ga gashin girarsu kadan ne, to idan aka yi wannan gyaran girar yakan fito da yanayin gira ya yi kyau tare da birgewa yayin kwalliya.

Ana yin irin wanan gyaran gira ne daidai yadda mace take bukatar yanayin girarta ya kasance. Akwai hanya ta farko da ake yin amfani da ita wajen aske gashin girar. Idan muka ce aski ba wai muna nufin aske gashin girar gaba daya ake yi ba. Abin da yake faruwa za ki sa reza  a rarrage gashin daga farkon girar mace zuwa karshe . Yawanci akan dan bar farkon gira da dan fadi. Ma’ana gashin zai yi dan yawa daga gaba.

Sannan sai a ci gaba da rarrage gashin da ke jikin girar har karshenta yadda za ta zama ‘yar sisiriya.

Idan aka samu yanayin girar ya yi yadda  ake bukata sai a rika yin amfani da jagira irin launin da ake bukata yadda  za a ja ta akan girar daidai yadda yanayin yadda girar ya kasance.

ADVERTISEMENT
Share