✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadakar kungiyoyin matasan Arewa sun goyi bayan Buhari a 2019

Hadakar kungiyoyin matasan Arewa ta nuna goyon bayanta ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sannan kuma ta bukaci ya sake fitowa takara a 2019 don karasa…

Hadakar kungiyoyin matasan Arewa ta nuna goyon bayanta ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sannan kuma ta bukaci ya sake fitowa takara a 2019 don karasa muhimman ayyukan raya kasa da cigabanta da ya faro fiye da shekaru biyu. 

Shugaban hadakar kungiyoyin, Hon. Mujahid Zaitawa shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Talatar da ta gabata a Abuja. Yana mai cewa babu wani dan takara a Najeriya da za a iya kwatanta kimarsa da ta Buhari, don haka suke fatan ya fito neman wa’adi na biyu, kuma ‘yan Najeriya a shirye suke su mara masa baya don karasa fitar da kasar nan daga bala’in da ya same ta tsawon shekaru.

“A cikin wadannan shekaru biyu na Buhari, ya nuna wa duniya cewa shi kwarzo ne kuma adalin shugaba, wanda yake aikata dukkan abinda ya fada. Kuma kyawawan ayyukansa ne suka sanya mu matasan Arewa dake cikin wannan hadaka nuna goyan baya gare shi. Kuma ko da ya ce ba zai tsaya ba, ‘yan Najeriya ba za su amince ba, zamu yi ta kiransa har sai ya amince.”

Hon. Zaitawa ya ci gaba da cewa, “Dukkan dan Najeriya nagari zai goyi bayan shugaba Buhari, domin ba kansa da iyalansa ne gabansa ba, kasar ce a gabansa. Kuma kafin zuwan Buhari komai a kasar nan ya lalace. Tabarbarewar tattalin arzikin kasa, tabarbarewar tsaro sannan da tsananin cin hanci da rashawa da ya mamaye kusan sannan ma’aikatun gwamnati. Amma daga hawansa ya saita komai yadda ya kamata. Sannan a da Najeriya ta na dogaro ne da man fetur, amma ya kirkiro harkokin noma don rage yawan dogaro da man fetur, a dalilin haka miliyoyin al’umma sun samu ayyukan yi, sannan kuma abinci ya wadata a kasa.”

“Sannan kuma ya maida hankali kan yaki da cin hanci da rashawa da fatattakar barayin gwamnati, a yau kowa ya shiga taitayinsa. Domin aiki ne ake yi babu sani babu sabo, kuma dukkan ‘yan Najeriya shaida ne akan haka. Haka kuma a bangaren tsaro ya taka rawar gani, inda cikin kankanen lokaci ya kawo karshen tada boma-bomai a kullu yomin da daruruwan ‘yan Najeriya ke mutuwa dare da rana. A kasuwanni da tasoshi da masallatai da coci-coci kashe mutane ake ba gaira ba dalili. Amma mun wayi gari duka wannan ya zama tarihi.

Da aka tambaye shi ko baya ganin fitowar manya-manyan ‘yan siyasa irin su tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso da tsohon gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamido za su kawo masa tarnaki a 2019? Sai ya ce ko alama, domin farin jinin Buhari ikon Allah ne, kuma babu wanda ya isa ya ja da ikon Allah, sannan ya ce Buhari kamar rana ne, idan ya fito tafin hannu ba ta tare shi.