✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya ci mutum 20 a Akure

A ranar Juma’ar da ta gabata ce ’yan Kasuwar Kayan Gwari da ke Mil 12 a Legas suka shiga alhinin rasuwar mutum 20 wadanda akasarin…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce ’yan Kasuwar Kayan Gwari da ke Mil 12 a Legas suka shiga alhinin rasuwar mutum 20 wadanda akasarin su ’yan kasuwar ne da suka shiga motakirar bas Homa a Tashar Boka da ke daura da kasuwar da zimmar zuwa gida Arewa bayan da suka ci kasuwar Karamar Sallah, inda suka gamu da ajalinsu a Jihar Ondo bayan da direban  wata babbar mota mai taya 12 ya ari hannunsu a yunkurinsa na kauce wa rami  inda suka yi taho-mu- gama nan take motocin suka kama da wuta, fasinjojin motar 19 da karamin yaro na goye suka kone kurmus.

Wakilin Aminiya ya ziyarci Tashar Boka da ke Kasuwar Mil 12 inda  motar ta dauki fasinjojin inda ya zanta da Mataimakin Shugaban Tashar Malam Kabir Abubakar Abdullahi wanda ya nuna alhininsa bisa faruwar lamarin tare da mika ta’azziya ga ’yan uwan mamatan. Kuma ya ja hankalin direbobi kan su kara natsuwa musanmman a lokutan da suka debi jama’a. Ya ce lura da lalacewar hanyoyin kasar nan akwai bukatar samun karin natsuwa a tsakanin direbobi. “Duk direba tukin mutum hudu yake yi, yana kula da gabansa da hagunsa da dama da kuma bayansa. Hanyoyin kasarmu sun tabarbare ko da yake a yanzu akwai wuraren da an dauko gyaran hanyoyin da dama haka kuma akwai wuraren da ba a zo kansu ba. Don haka dole ne direbobi su zama masu kula su rage gudu, yawan gudu shi ke janyowa idan aka samu hadari sai abin ya munana.  Dole direbobi su san inda ya kamata su yi gudu da wajen da ya kamata su lallaba, haka su ma fasinjoji su rika yin hakuri kada su rika azalzala wa direba domin kan ya yi gudu. Wani ma fasinja za ka ga ya dauko kaya fiye da kima duk irin wannan kadan ne daga kalubale da direbobi kan fuskanta. Tunda Allah Ya hukunta abincinmu na nan dole mu ratso wadannan hanyoyin to ya kamata a bi su a hankali sannan gwamnati ya kamata ta kara himma kan gyara hanyoyinmu na Arewa zuwa Kudu domin a samu saukin asarar rayukan da ake yi a kan hanyoyin sakamakon lalacewarsu,” inji shi.

Sani Boka shi ne matashin da ya yi wa motar lodi ya kuma yi rajistar matafiyan ya shaida wa Aminiya cewa fasinjojin mutum 19 maza ne matasa, sai wata mace guda dauke da danta a goye da suka yi hadarin, ya ce motar ta tashi daga Tashar Boka a Legas  da misalin karfe 6:30 na yamma sannan ta yi a hadarin ne a Jihar Ondo da misalin karfe 9:45 na dare. “Akwai wani direba da ya dauko tattasai shi ne ya shaida mana faruwar lamarin, ya ce shi ne mutum nA farko da ya isa wajen a lokacin da hadarin ya auku domin a wannan lokacin ya riske fasinjojin motar suna dago hannun suna neman dauki. Fatanmu Allah Ya karbi shahadarsu, Ya jikansu, Ya bai wa ’yan uwansu hakurin wannan rashin,” inji shi.

Aminiya ta zanta da wadansu direbobi a tashar ta Boka inda suka koka kan lalacewar hanyoyin kasar nan. Sun ce mafi yawan hadarin da ke lakume rayukan jama’a yana aukuwa ne sakamakon lalacewar hanyoyi, don haka suka yi kira ga mahunkunta da alhakin ya rataya a wuyansu su mai da hankali wajen gyaran hanyoyin domin rage salwantar rayukan al’umma a kan hanyoyin kasar nan.