✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya kashe dalibin Jami’ar Bauchi da wasu 2

Hadarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar wani dalibin jami’ar jihar Bauchi da ke Gadau. Dalibin mai suna Ibrahim Mohammed Karamba na ajin karatu na shekara…

Hadarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar wani dalibin jami’ar jihar Bauchi da ke Gadau. Dalibin mai suna Ibrahim Mohammed Karamba na ajin karatu na shekara ta biyu tare da wasu mutum biyu da hadarin ya rutsa da su.

Hadarin ya faru ne hanyar zuwa cibiyar jami’ar  da ke Yuli mai nisan kilomita 10 zuwa birnin jihar Bauchi kuma babbar hanyar zuwa Maiduguri.

Ibrahim Mohammed Karamba tare da wasu mutum biyu duk suna kan babur ne lokacin da wata mota kirar bas mai kujeru 18 tai kansu.

Daya daga cikin malaman jami’ar Dakta Mahmoud Ibrahim, ya bayyanawa wakilinmu cewa, hadarin ya faru ne a daidai kauyen Tirwun Kajitu kimanin nisan kilomita hudu zuwa hedkwatar jami’ar a Bauchi.