✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajara Isah ta bukaci ’yan jarida su rika yada labarai masu kyau game da Najeriya

Jaruma Hajara Isah ta bukaci kafafen watsa labarai na Najeriya su rika yada labarai masu kyau game da kasar nan, kamar yadda takwarorinsu da suke…

Jaruma Hajara Isah ta bukaci kafafen watsa labarai na Najeriya su rika yada labarai masu kyau game da kasar nan, kamar yadda takwarorinsu da suke sauran kasashen duniya suke yi.

Jarumar ta yi kiran ne lokacin da take tattaunawa da Aminiya a ranar Lahadin da ta gabata.

Jarumar ta ce abin takaici ne idan aka lura da yadda kafafen yada labarai a Najeriya ba su da wani abu da ya wuce yada munanan labarai game da kasar nan, inda hakan ba komai yake jawo ba, face bata wa kasar nan suna.

Ta ce, “Muna da abubuwa masu kyau a kasar nan wadanda idan kafafen watsa labarai suka watsa su, za su sauya tunanin mutane daga tunanin cewa babu wani abu mai kyau a cikinta.”

Hajara wanda ta fito a fina-finan Hausa na Ingilishi irin su ‘This’ the Way’ da kuma ‘There’s a Way’ ta amince cewa ana fama da talauci a Najeriya amma ya kamata ’yan jarida su rika yada abubuwan da kasar nan ke tinkaho da su ba wai munana ba.

Ta ce, “Abin takaicin ma shi ne yadda ’yan jarida suka zabi ko mayar da hankali wajen yada labarai marasa dadin ji game da Najeriya, na san ana fama da talauci a Najeriya ban kuma ce kada a yi labarin ba, amma me ya sa duk labaran da aka fi mayar da hankali gare su marasa dadin ji ne? Don haka ina kira ga kafafen watsa labarai na kasar nan su rika mayar da hankali wajen yada labarai masu kyau da za su dauki hankalin duniya don a daina yi mana kallon raini, sannan a dauke mu da daraja,” inji ta.