✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halin da ake ciki shekara uku bayan gano ma’adinin Nickel a Dangoma

Tun bayan gano ma’adinin Nickel da jaridun Daily Trust da Aminiya suka fara bayyanawa da kuma ci gaban da aka samu wanda har ila yau…

Tun bayan gano ma’adinin Nickel da jaridun Daily Trust da Aminiya suka fara bayyanawa da kuma ci gaban da aka samu wanda har ila yau jaridun suke bibiyar lamarin har zuwa watan Yunin bara, kawo halin da ake ciki kan yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a tsakanin al’ummar yankin da aka samu ma’adinin a filayensu da kamfanin da ke aikin hakar ma’adinin, wanda wani Bature dan kasar Austireliya ke gudanarwa.

Sai dai har zuwa yanzu da ake cikin shekara ta uku da bayyanar wannan ma’adinin, aikin ya dan tsaya tun karshen bara, bayan komawar Baturen kasarsa gabanin watan Disamba, abin da ake ganin sai bayan kammala zabubbukan da ake ciki kafin ya dawo; kamar yadda wadansu daga cikin mutanen garin Dangoma suka bayyana wa Aminiya a makon jiya a garin.

Malam Mahmud Suleiman shi ne Hakimin garin Dangoma kafin dakatar da hakimai da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi a wa’adinta na farko, kuma shi ne ke amsar dukan bakin da suka zo garin a hukumance kan harkar da ta shafi wannan ma’adini. Ya bayyana wa Aminiya cewa har yanzu dai aikin na tafiya a hankali.

“Aikin na tafiya a hankali amma tun bara da Turawan suka koma kasarsu don gudanar da bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara aikin ya tsaya cik. Yaranmu da ke aikin leburancin ma suka ci gaba da wasu harkokinsu sai dai muna ganin a yanzu tunda an gama harkokin zaben bana, wanda muke ganin yana daga cikin dalilan rashin dawowarsu a bana, za su fara haramar dawowa don gudanar da aikinsu” inji shi.

Malam Mahmud Suleiman, wanda shi ne Wamban Masarautar Kaninkon, wacce Dangoma ke karkashinta, ya nanata cewa kafin tafiyarsu sun sanya hannu kan irin abubuwan da za su yi wa mutanensu, kamar samar da wasu ajujuwan karatu da tsabtataccen ruwan sha da gyara hanyoyi da sauransu.

Shugaban Matasan Dangoma wanda kuma aka fara samun ma’adinin a gonarsa, Malam Isyaku Zamani Maduru ya ce baya ga ribar da za su samu daga ma’adinin, al’ummarsu ma za su amfana daga kudaden diyyar da gwamnati za ta biya kamar yadda aka yi yarjejeniya a tsakaninsu da Kamfanin Comet Mining, masu aikin hakar ma’adinin sannan bayan kammala aikin za a dawo musu da filayensu.

Zamani ya ce daga cikin yarjejeniyar akwai samar da wasu rukunin ajujuwa guda uku a yankuna uku da za su ci gajiyar aikin da aka samu ma’adinin da suka hada da Dangoma da Bakin Kogi da ke Masarautar  Nikyob (Kaninkon) da kuma Nindem da ke karkashin Masarautar Godo-godo dukansu a Karamar Hukumar Jama’a.

 Samfurin Nickel a Dangoma
Samfurin Nickel a Dangoma

“Da farko za su fara bayar da kashi hamsin ne na kudin da za a fara gina ajujuwan a shekara ta farko kafin a ci gaba da karkasa sauran kudade wajen tallafa wa dalibai biyan kudin jarrabawar fita daga sakandare na NECO da WAEC,” inji shi.

Shi ma ya ce aikin na gudana ne daki-daki kamar yadda kamfanin ya tsara tun daga shekarar 2014 zuwa shekarar 2040 kafin su kammala gaba daya.

“Dama na yi fata tare da  addu’ar Allah Ya ba wannan gwamnatin nasara a zaben da ya gudana domin ci gaba da aikinsa a wannan wuri, kamar yadda suka faro kuma su cika mana nasu alkawarin bunkasa tattalin arzikin kasarmu,” inji shi.

Baya ga ma’adinin na Nickel, akwai wasu ma’adinai da suka hada da Feldspar da wolfromite da graphite da tantalaye da gemstones da tin da columbite a yankin.