Search
Subscribe
Hana  bara a kan tituna a jihohi uku

Almajirai

Hana  bara a kan tituna a jihohi uku

Jihar Neja ta bi sahun jihohi biyu na Arewacin Najeriya wajen hana bara a kan tituna. Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Alhaji Muhammad Sani Idris ne ya fitar da wannan sanarwa Minna, inda ya ce hana barar ba ta shafi almajirai da suke karatun Alkur’ani Mai girma ba, ya ce gwamnati ta kafa kwamiti wanda zai sa ido wajen aiwatar da dokar ta hanyar da ta dace domin ganin ba ta samu nakasu ba kamar yadda aka saba yi a baya.

Alhaji Idris ya ce duk wanda aka samu yana bara a kan titi da sauran wurare za a kama shi sannan a gurfanar da shi a gaban kotu kamar yadda dokar  ta yi tanadi. Ya ce duk mai barar da aka kama shi kuma aka tarar ba dan asalin jihar ba ne, to za a maida shi jiharsa ta asali. Ya ce “Ba mu hana almajirai wadanda suke karatun allo ba amma ba za mu kale su ba zu a cikin  kwararo suna yawon bara ba.” Ya ce akwai hadin gwiwa a tsakanin gwamnonin Arewa kan yadda za a hada kai domin a yaki bara a kan titunan ta kowace hanya.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje shi ne Gwamna na farko da ya haramta bara a kan hanyoyin jihar a wannan lokaci. Ya bayyana haka ne lokacin da yake kaddamar da shirin bayar da ilimi a matakin farko ga kowa (BESDA) lokacin da ya raba takardun daukar aiki ga mutum 7,500 wadanda suka amince da aikin sa-kai a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, mako biyu da suka gabata. Ya ce “Wannan sabon tsarin da muka dauko zai ba almajirai sabon tsarin ilimi. Sannan su ci gaba da karatun u na haddar Alkur’ani Mai girma, kuma almajirai za su koyi  darasin Lissafi da Ingilishi.” Ganduje ya ce “Idan aka kama almajiri yana bara, ba wai an kama mai bara ba ne a’a za a kama mahaifan yaron ko masu kula da shi sannan mu tura su kotu saboda saba doka da suka yi.”

Gwamanatin Jihar Nasarawa  ma ta daura dan ba domin hana bara a fadin jihar. Gwamna Abdullahi Sule ya ce idan aka kama yaro yana bara iyayensa za a hukunta. A lokacin da yake kaddamar da dokar kula da ’yancin yara a Lafiya, ya ce iyayen da aka kama dansu yana bara za a hukunta su. Ya ce , “Wannan dokar bayan ta haramta bara a fadin jihar ta yi tanadi ga duk iyayen da muka kama dansu yana bara, to ba makawa su za mu hukunta  kan yadda suka wulakantar da amanar da take kansu suka bar ’ya’yansu suna bara a kwararo. Don haka gwamnati ta dauki mataki, domin daukar ’ya’yanmu a makarantun Tsangaya na (zamani) a kokarin magance matsalar.” Kamar yadda Gwamna Sule ya fada samar da kariya da tsaro da walwala da kula da lafiya da kuma nagartaccen ilimi  za su tabbatar cewa dukkan yaran sun samu wannan dama ta hanyar aiwatar da tsarin da aka bijiro da shi a fadin jihar na dokar kare hakkin yara ta shekarar 2005.

Wadannan jihohi uku na Arewa sun sanya dan ba na kawo karashen wannan al’amari na bara da bisa ga dukkan alamu yake yaduwa kamar wutar daji sannan wasu jihohi za su yi koyi da irin wannan mataki. A matakin farko al’amari ne mai kyau, amma ga dukkan alamu ana tuya ana mantawa da albasa, domin hukumomi suna daukar matakai ba tare da suna gayyato dukkan masu ruwa- da-tsaki ba. Bara ga yara kanana a Arewacin Najeriya al’amari ne mai sarkakiya, mafi yawa daga cikin matalauta a kauyyuka sukan hada ’ya’yansu da malamai  domin su koya musu karatun Alkur’ani a garuruwa masu nisa.  Tsarin da ake bi na karatun allo ya dauki shekaru masu yawa ana gudanar da shi, amma da an dauki matakin gyara tun farko da yanzu an shawo kan al’amarin.

Haka kuma muna mamaki ko tsare yara kanana domin hana su  bara a kan tituna zai kawo gyara a tsarin. Domin duk wadannan yara an baro su ne daga gidajensu zuwa birane ba tare da wani tsarin muhalli ko tsarin ciyarwa ba. Don haka sun zama su ne laifi yake fada wa kansu. Alhali asalin masu laifi su ne iyayensu da kuma malamansu. Hanya mafi sauki ita ce a kama duk wani malami da ya dauko yaro daga wajen iyayensa zuwa birni, a tilasta musu su mai da wadannan yara ga iyayensu, sannan a yi musu barazanar dauri da zarar sun sake kawo wani yaro zuwa birni da sunan karatu. Wannan ita ce hanya mafi sauki da za a magance wannan matsala. Mataki na gaba kuma sai a samar da kayyakin aiki na koyarwa da kuma samar da tsarin ilimin addini da na zamani, a samar da wadannan wurare a dukkan garuruwa ta yadda ba wanda zai bada uzurin turo dansa yawon almajiranci. Wannan mataki tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Aliyu Magatakarda ya taba gwadawa a lokacin mulkinsa. Wannan ita ce hanya mafi kyau da ya kamata a bi.

 

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin