✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyi kariya daga ambaliyar ruwa

A makon da ya gabata, an samu ambaliyar ruwa a garuruwan Arewa da dama, wadda take kokarin sanadiyyar rasa rayukan al’umma da dukiya mai dimbin…

Tambarin fadakarwa game da Ciwon Daji Na MamaA makon da ya gabata, an samu ambaliyar ruwa a garuruwan Arewa da dama, wadda take kokarin sanadiyyar rasa rayukan al’umma da dukiya mai dimbin yawa. Dama hukumomin binciken yanayi na kasar nan sun bayyana cewa za a iya samun ruwa mai yawan da zai iya yin gyara (barna) kuma sun yi hasashen cewa za a iya ci gaba da samun irin wannan ruwa mai karfin gaske, don haka ya zama wajibi a ci gaba da daukar matakai na kariya ko a rage yawan salwantar rayuka. Shi ya sa za mu dauki wani dan fili mu zayyana hanyoyin kariya kafin mu amsa tambayoyin masu karatu.
Masana sun tabbatar da cewa saboda karin samun dumamar yanayi wanda kan sa kankarar cikin manyan tekunan duniya narkewa, wanda hakan kuma kan sa tekun ya cika ya batse, ta yadda koramu da rafuka su ma sukan ciko sosai, ya sa magudanan ruwanmu suka ki kwaranyewa. Wannan a inda magudanan suke da tsabta ma ke nan. A mafi yawan garuruwanmu, magudanan ruwan ba ma ruwa ne ya cika su ba, shara ce ta cika su. A wasu wuraren ma ba ka ce hukuma ta taba haka magudanar ruwa a wurin ba.
Ga aikin ginin gidaje da kaburbura na laka. To ita dama laka ai abokiyar ruwa ce. Masu karatu ba za su yi mamaki ba idan suka ji cewa har gobe akwai masu gina gidan laka a cikinmu ba. Kai yanayin yadda muke gina kaburburanmu ma dole ne su canza idan dai muna so mu kiyaye annoba saboda a yanzu ruwa har tono gawarwaki a makabartu yake.
Za a lura cewa tun zamanin da nasara ya zo kasar nan shekaru aru-aru da suka shude, bai taba yin ginin laka ba sai na dutse, wanda shi ba abokin ruwa ba ne. A yanzu haka ma wuraren fasa dutse a kasar nan ’yan China sun mamaye su, mu kuma mun cika wuraren tono kasa, wanda yakan sa wurin ya yi rami ruwa ya cika su, su jawo mana sauro da sauran kazanta. Don haka idan aka karanci yawancin sababin ambaliyar ruwa cikin basira, za a ga laifinmu da na hukumominmu a ciki ya fi yawa kuma ta wadannan sababi za iya gano hanyoyin kariya cikin sauki kamar haka:
1-A daina zuba shara cikin magudanan ruwa da hukumomi suka samar.
2-Su kuma hukumomi su rika gina rufaffun magudanan ruwa, ba budaddu ba, domin shara cika budaddun take. Sa’annan a ware masu kula da su na musamman, kamar yadda aka ware masu share tituna.
3-Idan an samu mutanen unguwa sun yashe magudanan ruwa, sun jibge sharar a gefensu, dole hukumomi su kwashe cikin gaggawa; kada sharar ta koma magudanan ruwan.
4-A guji gina muhalli a kwari ko wata hanyar ruwa ko da a lokacin da aka yi ginin babu ruwa a ciki.
5-A guji gina muhalli da laka kawai.
6-Dole a kara wa laka siminti ko yaya ne a wajen gina kaburbura.
7-Jama’a su tabbatar sun gyara muhallansu a ranakun da aka ware na Asabar din karshen wata, ba su yi zaman shantakewa a gidajensu ba.
8-Hukumomi kuma su dawo da aikin masu duba-gari domin tabbatar da cewa an tsabtace ko’ina.
Tambayoyin wannan makon:
Ko akwai wani magani da za a shafa a jikin fata idan mutum ya ji rauni ko ya kone domin wurin ya dawo daidai?
Daga Hamza, Jihar Neja
Amsa: Ban san ko kana nufin maganin tabo ba, wato maganin da zai sa mutumin ya ji rauni ko kuna ya nemi tabon ciwon ya rasa bayan ciwon ya warke. E, kwarai kuwa za a iya samu, duk matar da ka tambaya ma ai za ta iya ba ka sunan wannan magani. Man shafawa ne masu tsada, masu dauke da sinadaran bitaman na rukunin A da E da sauran sinadaran gyara fata irinsu collagen da sauransu. Kai, a jikin wadannan man ma zaka ga an rubuta da Turanci cewa maganin warkar da tabo ne. A likitance ba su da wata illa idan ba su dauke da sinadaran sa bilichin ko guba, wato irinsu mercury da lead. Za a iya gwadawa a gani idan an ga suna kwaile fata a ajiye.
Ka san dama ai shi tabo a mafi yawan lokaci ba wai kin warkewa yake ba, daukar lokaci mai tsawo kamar shekaru yake kafin ya warke. To, su irin wadannan kayan shafawa suna rage tsawon lokacin da za a dauka tabo ya baje, daga shekaru zuwa watanni. Idan ka ga ciwo ko tabo ya ki warkewa to ko dai yana bukatar dinki ba a yi ba, ko yana bukatar magani ba a sha ba (kamar na kashe kwayoyin cuta), ko yana bukatar wasu sinadarai na abinci ba a ci ba, ko kuma tabon kato ne wato ya ci fata sosai.
Idan na yi bayan gida na gama, wani abu yakan fito a karshen fitsarina fari mai kauri. Na je asibiti an min gwajin jini da fitsari ba a ga komai ba, an ba ni magunguna da allurai har yanzu ban daina ba. Mece ce shawara?
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Amsa: To ai dama idan ba ka da sauran alamomin ciwon sanyi kamar zafin fitsari, yawan fitsari, dan zazzabi ai ba kwayoyin cuta ba ne. Ga shi ma an gwada fitsarin ba a ga komai ba. Sun dai ba ka magungunan ne don a faranta maka rai, amma ba ka bukatarsu. Wannan farin ruwa bayan mutum ya yi nishin bayan gida ba ciwo ba ne, shi ne wanda malamai suke kira wadiyyi, mai kama da maniyyi, amma bayan fitarsa ba sai an yi wanka ba, mu kuma mu kira shi prostatic secretions..

LAFIYAR MATA DA YARA

Hanyoyin Kariya Daga Ciwon Daji Na Mama

Ciwon daji na mama shi ne ma ya fi kama mata fiye da na bakin mahaifa. To tun da mun yi bayanin na bakin mahaifa a wancan mako, bari mu yi bayanin yadda za a kare kai daga na mama.
Wannan ciwo shi kuma akasin na ciwon dajin bakin mahaifa ne. Mun ce ciwon daji na bakin mahaifa ya fi shafar mace da ta yi aure-aure da yawa, ko ta haihu da yawa. Shi kuma wannan ya fi kama matar da ta dade ba ta yi aure ba ko ta dade ba ta haihu ba, ko wadda ba ta taba shayarwa ba. Duk da wadannan din kuma, matar da mahaifiyarta ta samu ciwon ta fi kowa shiga hadarin kamuwa. Sai kuma mace mai kiba, sai mai yawan shan kwayoyin kayyade iyali wato pills.
Alamomin ciwon sun hada da ganin kullutai ko fitar jini a kan maman maimakon ruwan nono. Kai duk wani abu sabo da mace ta gani ba ta yarda da shi ba a kan mamanta, dole ta dau matakin zuwa a duba.
Ta yaya ake kare kamuwa daga ciwon daji na Mama?
1-Babbar hanyar kare kai daga kamuwa daga kansar mama ita ce ta shayarwa, domin akwai matan da za su haihu amma ba su son shayarwa. Wato masana sun yi amanna cewa shayar da yaro a kalla tsawon shekara biyu yana iya kare mace daga kansar mama. Haka nan kuma yawan yaran da matar ta shayar, yawan kariyar ke nan.
2-Sai kuma rage kiba, wato a rage maiko a abinci, a rika kuma yawan motsa jiki.
3-Sai rage shan kwayoyin nan na ba da tazarar iyali wato, pills. Idan da hali ke nan, gara a bi wasu hanyoyi ba ta wadannan kwayoyi ba.
4-Duk matar da ta kai a kalla shekaru arba’in, yana da kyau ta koyi yadda ake duba mama. Wannan wata hanya ce da mace za ta bi ita kadai a dakinta ko ita da mai gidanta domin duba mamanta a mudubi ko akwai wani sabon kari a jiki.
Yadda ake yi kuwa shi ne: Mace ta tube, ta sa katon mudubi gaba ta dora hannayenta kan kugunta, ta duba ta ga ko akwai wani yanayin canjin fata ko wani kullutu ko kari a jikin mamanta. Bayan ta gama sai ta juya gefe, ta sake yin haka (wato ta duba gefen dama da hagu). Daga nan sai ta sake kallon mudubin, ta sa hannunta na hagu a bangaren dama, ta fara latsa gefe zuwa ciki, kasa zuwa sama, har karkashin hammata, ta ji ko za ta ji wani kullutu. Sai ta sake dawowa kan maman ta matso shi ko za ta ga wani ruwa ya fito (idan ba shayarwa take ba ke nan). Idan ta gama sai ta je bangaren hagu ta yi kamar yadda ta yi a dama. Idan babu komai shi ke nan ta gama sai bayan akalla wata shida kafin ta sake. Amma idan ta ji wani kullutu ko ta matso wani kalar ruwa, to dole sai ta je asibiti an kara bincike.
A mafi yawan lokuta idan aka ji kullutu ko kurji, ba kansa ba ne, kari ne wanda da an yanke shi shi ke nan.