✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyin da za a bi don magance warin gashin kai

Warin gashin kai yana daya daga cikin abubuwan da ke ta da wa mata da dama hankali. Sai a ga mace ta yi ado ta…

Warin gashin kai yana daya daga cikin abubuwan da ke ta da wa mata da dama hankali. Sai a ga mace ta yi ado ta fita amma ana jin wari. Ba wani abu ba ne illa warin da ke tashi daga gashinta. Saboda matsalar fata na janyo warin gashin kai. Yawan sanya man gashi na dada warin gashi musamman idan man ya yi yawa a gashin kuma ya hadu da ruwa ya fara wari. Yawan barin gashi ya yi datti sosai ma na janyo warin gashi.

• Idan za a sayi man wanke gashi a sayi wanda ke dauke da sinadarin sulphur ko zinc ko mai dauke da anti-bacterial.

• Man wanke gashin kai mai dauke da sinadarin silicyl na magance wadannan matsaloli.

• Za a iya amfani da lemun tsami domin magance warin gashin kai. Bayan an wanke gashin da man wanke gashi, sai a matse lemun tsami a hada da ruwa sai a yi wa gashin wankin karshe.

• Ruwan tumatir na magance warin gashin kai. Kafin a wanke gashi da man wanke gashi, a matse ruwan tumatir sai a shafa a fatar kan. A jira na tsawon minti 10 kafin a wanke da man wanke gashi.

• Ana iya hada ruwan ganyen dogon yaro a cikin man wanke gashi sannan a juya su sosai kafin a fara amfani da shi yin hakan na rage warin gashin kai.

• Za a iya samun man gashin kai da ke dauke da man labender domin samun kamshin gashi a koyaushe.