✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyin magance Satar Zati

Daga bayanan da suka gabata, mai karatu ya fahimci abubuwa da dama da suka shafi wannan tsari na ta’addanci. Musamman tun daga ma’anar wannan ta’ada…

Daga bayanan da suka gabata, mai karatu ya fahimci abubuwa da dama da suka shafi wannan tsari na ta’addanci. Musamman tun daga ma’anar wannan ta’ada da nau’uo’insa da hanyoyin da masu aiwatarwa ke bi wajen aiwatar da aika-aikansu, har zuwa alamomin da ke nuna an sace wa mutum zatinsa sanadiyyar sace bayanansa da aka yi. Wadannan bayanai manuni ne kan cewa kafin masu wannan al’ada mummuna su ci galaba a kan mai bayanan, sai da shi kansa ya yi sakaci da su, ko wadanda ke rike da bayanan nasa suka yi sakaci da su. Wannan ke nuna akwai bangarori biyu muhimmai da ’Yan Dandatsa ke bi wajen samun wadannan bayanai.

bangaren farko shi ne ta hanyar mai asalin bayanan. Misali, a ce an sace shafinka na Facebook, ana hawa kai-tsaye, ana rubuta shegantaka iri-iri ba tare da sani da kuma amincewarka ba. Zai iya yiwuwa daga sakacinka ne aka samu kalmar izinin shiganka, wato: “Password,” ko kuma an yi kirdado har aka dace da kalmar da kake amfani da ita a matsayin mabudi. Wannan bangaren farko ke nan. bangare na biyu shi ne, ta hanyar wanda aka bai wa bayanan ajiya, sanadiyyar huldar kasuwanci, ko aikin gwamnati, ko wata mu’amala ta musayar bayanai. Misalin wannan shi ne a ce kana da akwatin Imel na kamfanin Google (Gmail) ko Microsoft (Hotmail), sai wadansu ’Yan Dandatsa suka barko cikin rumbun adana bayan kamfanin Google ko Microsoft, suka kwashe bayanan mutane kai-tsaye; adireshin Imel dinsu da kalmomin iznin shigarsu baki daya. Ko a ce kana aiki da wata ma’aikata ta gwamnati ko kamfani, kuma sun karbi bayananku sun zuba a rumbun adana bayanansu da ke kamfanin ko gidan yanar sadarwarsu, sai ’Yan Dandatsa suka barko cikin kwamfutocinsu, suka kwashe wadannan bayanai kai-tsaye. Wannan ita ce hanya ta biyu.

Ko ma ta wace hanya ce, akwai dayan dalilai biyu da ke faruwa har haka ta kasance. Ko dai ya zama sakaci ne daga mai asalin bayanan ko kuma daga hukuma ko kamfanin da ke adana bayanansa. Ko kuma tsantsar kwarewar ’Yan Dandatsar ne da kuma kaddarar Ubangiji, wacce ta riga fata. Dalili na biyu ba mu iya komai a kansa, domin duk dabararka, mai son kayanka ya shallake ka. Amma dalilin farko wajibi ne mu dube shi. Ta wace hanya mai karatu zai iya tsare bayanansa ba tare da wani dan Dandatsa ya samu kaiwa gare su cikin sauki ba?  

Sannan idan har aka samu kaiwa ga bayananka har aka aikata ta’addanci da su, wace hanya za ka bi wajen kare kanka, musamman mu da muke nan Najeriya? A kasashe irin Amurka inda suke da tsari na musamman ga mutanen da aka yi musu irin wannan ta’addanci, matsalarsu kadan ce. Amma a Najeriya, babu wani tsari na musamman da hukuma ta tanada ga wadanda aka sace bayanansu har aka aikata ta’addanci da su. Dole ne ka san hanyar da za ka bi wajen ganin ka bai wa kanka kariya da kariyar Ubangiji, gabanin mummunan sakamakon abin da aka aikata ya tunkare ka.

 

Kariya gabanin aukuwar matsala:

A matsatinka na wanda ke da bayanai a wasu gidajen yanar sadarwa na zamani, inda ake ba ka damar isa gare su don wata maslaha ta rayuwarka, dole ne ka tanadi hanyar kariya ga wadannan bayanai.  Haka idan hukuma ce ko wata ma’aikata, dole ne ta tanadi na’urori da manhajojin da za su bai wa bayanan jama’a kariya. Domin wannan zai taimaka wajen kare mutuncin ma’aikatar da kuma kimar ma’aikatanta. Idan bayanan suna adane a kwamfutocin da ke ma’aikatar ne, dole ne a tanadi na’urorin kariyar bayanai. A bai wa kwamfutocin da ke dauke da su kariya ta zahiri da kuma kariya ta ma’ana. Har wa yau, hatta harabar hukuma ko ma’aikatar, dole ne a sanya kariya. A lika na’urorin daukar bidiyo na dukan abin da ke gilmawa daga waje zuwa cikin ma’aikatar a kowane lokaci. Sannan a cikin ginin ma’aikatar ma inda sauran ofisoshi suke, dole ne a tanadi irin wadannan na’urori na daukar hoto. Sannan a tsakanin kwamfutocin da ke dauke da bayanan da kuma sauran kwamfutoci, su ma dole ne a tanadi na’urar da za ta rika lura da nau’in sadarwar da ke aukuwa a tsakanin kwamfutar da sauran kwamfutocin ma’aikata. Musamman na’urar da ake kira: “Intrusion Detection System” ko “IDS” a gajarce.  Na’ura ce, kuma manhaja ce da ke gane kowane irin kutse da ka iya aukuwa tsakanin ma’adanar bayanai da mai son isa gare su.

Idan bayanan ba ma’aikatar suke ajiye ba, suna dauke ne a gidan yanar sadarwa, nan kuma dole na farko ya zama kamfanin da zai gina shafin amintacce ne. Haka kuma, a samu tsarin kariya a shafin gidan yanar sadarwar, don hana masu yunkurin isa ga bayanan da ke ciki isa gare su. Akwai tsarin kwakulo bayanan da ke rumbun adana bayanai a gidan yanar sadarwa da karfin tsiya mai suna: “SkL Injection.” Da yawa cikin ’Yan Dandatsa kan yi amfani da wannan hanya wajen sansanowa da kwakulo bayanai ta hanyar fom din ake tanadawa don karbar bayanan mutane. Hanyar mai sarkakiya ce kuma mai hadari.

A bangarenmu na daidaikun jama’a kuma, hanyoyin da za mu iya bai wa bayananmu kariya dai bai wuce ta zabar kalmar sirri “Password” nagartacce ba. To amma tsarin Satar Zati bai takaitu ga “Password” kadai ba. Suna bibiyar “Password” ne don ita ce kofar isa ga bayanan. Hakikanin manufar ita ce samun damar isa ga bayanan. Sauran dalilan sun shafi yadda muke mu’amala da jama’a shafukan sada zumunta da yadda muke yada bayanmu da irin mutanen da muke karba abota da sauransu. A nan za mu fara bayani ne kan yadda ake zabar “Password,” da sauran abin da ya shafi kariya ta wannan fanni. A gaba kuma sai mu kawo bayanan kariya da suka shafi sauran hanyoyin mu’amala a Intanet. Bari mu fara da ma’anar kalmar “Password,” me take nufi?:   

Ma’anar kalmar ‘Password’:

Sabanin yadda na saba a baya, ga duk wanda ya saba karanta rubuce-rubucena kan batun Intanet da hanyoyin mu’amala da wannan fasaha, ya san na saba amfani da: “Kalmar izinin shiga” ne, don nufin kalmar “Password.” Sai dai a wannan karo zan yi amfani da kalmar Ingilishi ne, saboda wasu dalilai na zahiri. Kalmar “Password” wadda nake kira da suna: “Kalmar izinin shiga,” na nufin: “Kalma ce ko jerin haruffa da lambobi da alamomin rubutu da ake amfani da su wajen tantancewa ko tsaro ga wasu bayanai kafin kaiwa gare su, ta hanyar na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani.” Abin da wannan ke nufi shi ne: ma’anar kalmar “Password” na nuna abubuwa ne kamar haka: (1) Akwai kalma (misali: “Abdullahi” ko “Ibrahim”) ko haruffa da ke cakude da lambobi ko alamomin rubutu (misali: “isa1980” ko “ali4389” ko “audu32&&”).  (2) Amfanin kalmar shi ne tantance wasu bayanai da ke tsare a wani mahalli. (3) Ana amfani da “Password” ne a kan na’urori da hanyoyin sadarwa da ke da sila da wata kwamfuta mai dauke da bayanan da ake son kaiwa gare su, ko kuma kwamfutar da ke dauke da bayanan kai-tsaye.

Asali da tarihin “Password”:

Malaman tarihi a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani sun yi ta kokarin nemo hakikanin “Password” din farko da aka fara amfani da ita a duniya, amma abin ya ci tura. A tare da haka, tarihi ya hakaito sa’ar da ake zaton an fara amfani da wannan tsari ne don tantance tsarin isa ga bayanai da ke cikin wata ma’adana ta na’urar sadarwa ta zamani. Bayanai sun nuna cewa wannan tsari ya samo asali ne tun farkon zamanin samuwar kwamfutoci shekara sama da 60 da suka gabata. Babbar cibiyar binciken kimiyya ta kasar Amurka mai suna “Massachusetts Institute of Technology,” (MIT) ta samar da wata kwamfuta a 1961 mai suna: CTSS, wadda ke amfani da wata babbar manhajar kwamfuta mai suna: “Time Sharing System” (TSS).