Har yanzu talakawa ba su gani a kasa ba – Abba Anas 

Alhaji Abba Anas Shugaban Jam’iyyar SDP ta Jihar Jigawa

Shugaban Jam’iyyar SDP na Jihar Jigawa Alhaji Abba Anas Adamu, ya bayyana cewa har yaznu talakawan Najeriya ba su gani a kasa ba a wannan gwamnati ta Jam’iyyar APC. Kuma ya rashin gamsuwa kan rashin sashihancin zaben kananan hukumomin da jiharsa ta gudanar:

 

A matsayinka na dan siyasa yaya za ka kwatanta karo na biyu na wannan mulki da aka shiga?

To da farko dai a fahimtata ina ganin kamar mutum ne yana cin abincin safe sai kuma ya koma yana kallon abincin da za a dafa da rana. Don haka ka ga akwai kwadayi da zari a cikin lamarinsa. Sannan na biyu a siyasance ba a kula da abubuwan da ya kamata a kula da su wadanda za su amfani talaka su inganta rayuwa al’umma ba. A yanzu an fi mayar da hankalin kan dangantaka ta siyasa da siyasar ubangida, ta yadda a kullum abin da suka sanya a gaba shi ne yadda za su gyara wannan dangantaka tasu amma ga shi an yi biris da maganar al’amuran da suka shafi lafiyar talakawa inda za ka ga asibitota an bar su babu magani babu likitoci. A inda za ka ga majinyata sun ninka likitoci yawa. Haka abin yake a bangaren ilimi inda har yanzu za a samu dalibai tare da malamansu suna barci a karkashin inuwar bishiya.

 

ADVERTISEMENT

A wane sikeli za ka iya dora wannan gwamnati?

A gaskiya sun kasa cika alkawurran da suka yi wa mutane. Don haka zan iya cewa sun kasa. Yanzu idan ka dauki maganar tsaro kuma ka dubi abin da gwamnatin baya ta yi sannan ka kalli abin da wannan gwamnatin ke ikirarin ta yi za ka ga ba ta sauya zane ba. Domin a yanzu da nake magana da kai kusan rabin Jihar Borno na hannun ’yan Boko Haram.

To ganin zubin da Shugaban Kasa ya yi na sababbin ministocinsa da yadda ya dauki Ma’aikatar Tsaro ya ba tsohon Janar na soja ba ka ganin haka na nufin karshen duk wani kalubale da kasar nan take fuskanta ya zo?

To shi da wanda yake kan kujerar ba tsohon sojan ba ne? Ai matsalar ita ce har yanzu akwai hafsoshin sojan da a da su ne suke jan ragamar sojan kuma sun kasa kawar da wannan matsala ta tsaro kuma har zuwa yanzu su ne a kan kujerar. Ya kamata a ce an sallame su tunda ba su san aikinsu ba. Kuma kowa ya san sun gaza don haka ina ganin ya kamata Shugaba Buhari ya sauke wadannan manyan hafsoshin sojojin kasar nan, a yi sabon zubi a gwada a gani ko Allah zai taimaka a shawo kan matsalar tsaron da ta-ki-ci-ta-ki cinyewa.

 

Gwamnati ta fito da karin harajin kayan bukatun yau da kullum (BAT), Babban Banki ya fito da tsarin cajin kudi don jiya ko cire wani adadin kudi, kana ganin wannan zai taimka a fannin tattalin arziki ko su talakawa?

A gaskiya babu yadda za a yi ka sanya irin wadannan matakai ba tare da ka kawo wa jama’a ko shi mai biyan harajin wata kafa da zai samu wata moriya daga wannan haraji da ka dora masa ba. In ka shekara sanya irin wadannan matakai kamar na rufe kan iyakokin kasar nan ba tare da ka samar da hanyoyin da abinci zai yalwata ba a cikin kasa, to kamar kana irin abin nan ne da ake cewa da kare ana biki a gidansu, ya ce to ya gani a kasa.

Don haka har yanzu talakawa ba su gani a kasa ba, domin talauci yana kara karuwa ne a cikin al’umma a yanzu. Ka dubi maganar mafi karancin albashi na Naira dubu 30 har yanzu an kasa fara biya a matakin tarayya ballantana a jihohi duk da cewa wasu jihohi sun yunkura sun fara biya, amma har yanzu tana kasa tana dabo.

Amma idan na dubi kokarin da Shugaban Kasa yake yi nna samar wa kananan hukumomi ’yanci ta hanyar  ba su kudinsu kai-tsaye dole a yaba masa. Don ta haka ne za a samar wa talakawa wasu muhimman ayyuka.

 

Yaya maganar zaben kananan hukumomin da Jihar Jigawa ta yi?

Zabe dai an yi zabe, amma ya bar baya da kura, domin bayan mun yi nazarin dokar da majalisa ta yi da dokokin hukumar zabe, sai muka gano akwai matsala wajen da aka ce wai duk wanda zai tsaya takarar shugaban karamar hukuma sai ya biya Naira dubu 500, kuma wanda zai tsaya takarar kansila sai ya biya Naira dubu 200 na sayen fom. Wannan a binciken da muka yi ya saba wa doka domin mun gano cewa in dai wanda ya tsaya takarar majalisar jiha bai biya komai ba, wajen sayen fom haka shi ma wanda zai tsaya takara a karamar hukuma bai kamata ya biya komai ba. Don haka wani shiri ne kawai jam’iyya mai mulki ta yi tare da hadin bakin wasu jam’iyyun adawa don a hana wadansu ’yan takara na wasu jam’iyyu su tsaya.

 

Wane kira kake da shi ga gwamnatin Shugaba Buhari da gwamnatinku ta Jihar Jigawa?

A gaskiya yanayin da ake tafiyar da shugabanci a kasar nan, yana bukatar a yi gyara a kai ta kowane fanni ka duba.

Harkar tsaro babu wani ci gaba da aka samu, haka a fannin ilimi, ga talauci a tsakanin al’umma uwa-uba yadda al’amura suke tafiya ya kamata gaskiya Shugaban Kasa ya hanzarta daukar mataki na sauwaka wa al’umma halin tsananin da ake ciki, ba wai don ina wata jam’iyya ba. Koda a Jam’iyyar APC nake dole ne mu gaya wa kanmu gaskiya, akwai gyara a tafiyar wannan gwamnati tun daga matakin tarayya har kan gwamnatinmu ta Jigawa.

 

 

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya