Search
Subscribe
Haramta Kungiyar IMN: Gwamnati da ’yan Shi’a sun sake sa zare

Sufeto Janar na ‘Yan sandan Najeriya Muhammad Adamu

Haramta Kungiyar IMN: Gwamnati da ’yan Shi’a sun sake sa zare

A makon nan ne Gwamnatin Tarayya ta haramta Kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) ta ’yan Shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Yakub Zakzaky, bayan da wata Babbar Kotu ta yanke da hukuncin haka. Sai dai tsugune ba ta kare ba, domin kuwa mabiya kungiiyar, ta bakin daya daga shugabanninta, sun ce ba za ta sabu ba, a yayin da  gwamnati ta dauki alwashin tabbatar da aiki da hukuncin kotun.

Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ne ya ayyana haramta kungiyar, inda ya ce za su dauki kungiyar ta IMN a matsayin kungiyar ’yan ta’adda kamar yadda kotu ta hukunta. “Game da ayyana Kungiyar IMN ta ’yan Shi’a a matsayin kungiyar ta’addanci da hukuma ta yi, duk wani mutum da yake ciki ko yake mu’amala da kungiyar ko ya sanya hannu a cikin wasu harkokinta, za a dauke shi a matsayin dan ta’adda,” inji Sufeto Janar din.

Ya ci gaba da cewa duk wanda ake tuhuma da wadannan ayyuka na ta’addanci za a gabatar da shi a gaban kotu, a tuhume shi a karkashin dokar da ta hana ayyukan ta’addanci. Ya bayyana haka ne a wani taro da ya jagoranta da manyan jami’an ’yan sanda a hedikwatarsu ta kasa da ke Abuja.

“Kungiyar IMN ta mabiya Shi’a da Sheikh Zakzaky yake jagoranta, wacce ba ta amince kuma ba ta da’a ga Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, a yanzu a hukumance an ayyana ta a matsayin kungiyar ta’addanci,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa “Don karin bayani, ya kamata mutane su sani cewa Najeriya kasa ce mai bin tsarin sekulanci, wacce take da kundin tsarin mulki, wanda shi kuma ya ba da dama ta bin duk addinin da mutum ke so. Amma fa za a iya yin hakan ne tare da yin taka-tsantsan wajen abubuwan da ka iya kawo barazana ga tsaron kasa.”

Ya ce, “Muna nanata cewa dukkan ’yan Shi’a za su iya ci gaba da yin addininsu tare da samun cikakken tsaro, domin babu wata kotu da ta hana su yin haka.”

Ya ce ayyukan wannan haramtacciyar kungiya ta IMN sun yi kama da ayyukan ’yan tawaye, kuma hakan ka iya jefa kasa cikin fadan addini. “Ayyukansu sun saba wa Kundin Tsarin Mulkin kasar nan, sashe 1(2) (A) da (B) na bangaren hana ta’addanci, na 2013 da kuma sashe na 2(1) (A) (B) (C) na hana ta’addanci na 2013 wadanda duk suka fayyace matsayar tsaron kasa,” inji shi.

Da yake magana game da ayyukan Kungiyar IMN da suke saba wa doka da oda, Shugaban ’Yan sanda cewa ya yi “Suna da alaka ta kut-da-kut da wasu kasashe wadanda suke ba su tallafi da horo domin su tayar da zaune-tsaye a nan kasar.

“Suna kafa shingaye suna tare hanyoyi tare da kaddamar da hare-hare a kan jami’an tsaro da kuma kafa runduna ta jami’an tsaronsu na kansu, wadanda suke kira da ‘Hurras’ wadanda suke kuntata wa jama’a da su. Haka kuma suna da tutarsu da sojansu kuma suna yin ayyukan atisaye, inda ta kai ma sun kafa wata kasa tasu ta kansu,” inji shi.

Ra’ayin kwararru kan tsaro

Tsohon Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Mike Ejiofor, ya ce kamata ya yi gwamnati ta ci gaba da tattaunawa da ’ya’yan Kungiyar IMN. Ya ce “Kamata ya yi a samo hanyoyin lumana don warwar rikicin.”

Ya yi gargadin cewa idan aka bari har su ma suka fara buya kamar yadda ’yan Boko Haram suke yi a yanzu, to gwamnati ba za ta samu wadanda za ta tattauna da su ba.

Shi kuma Shugaban Kungiyar ASIS, mai bin kadin al’amuran tsaro, reshen Abuja, Kabir Adamu cewa ya yi “Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da wani reshe nata wajen kawo karshen wannan lamari da ya dade yana ci wa kasar nan tuwo a kwarya. Wannan wata babbar hobbasa ce. Barin lamarin a yadda yake tafiya a baya babban kuskure ne.”

A lokacin da yake magana da Aminiya, Okechukwu Nwanguma, Babban Daraktan Kungiyar Wayar da Kan Al’umma Game da Tsaro (RULAAC), ya ce ayyana kungiyar a matsayin ta ta’addanci ba zai haifar da da mai ido ba. Ya ce “Wannan ya saba wa abin da ita kanta gwamnatin take yi na rashin bin doka da oda. Kamata ya yi gwamnati ta bi umarnin kotun da ta umarce ta kan ta saki jagoran kungiyar wato Zakzaky da matarsa kuma ta dauki nauyin duk wani ba daidai ba da aka yi musu.”

Shi kuwa Lauyan Kungiyar IMN ya ce kungiyar za ta garzaya kotu domin kalubalantar hukuncin da kotu ta yi na haramta ta. Ya ce ba a ba su damar kare kai ba a lokacin gudanar da shari’ar.

“Saboda haka Kungiyar IMN tana da mafita ko dai kotu ta saurari korafinsu a bisa wa’adin da aka tsayar, tsakanin kungiyar IMN da bangaren gwamnati ko kuma muna da damar daukaka kara.

“Wannan hukunci, Kungiyar IMN tana da damar daukaka kara zuwa kotun gaba domin bayyana dukkan wasu hujjojin da muke da su bisa rashin ingancin odar da kotu ta bayar na haramta mana dukkan harkokin kungiyar,” inji lauyan.

Mai magana da yawun Kungiyar IMN, Abdullaahi Musa ya ce “Gwamnatin Tarayya ta fara bin umarnin kotun farko na sakar mana malaminmu, Ibrahim Zakzaky kafin a bayyana odar da take haramta kungiyar.

“Babu wani wanda ya isa ya hana mu yin addininmu. Suna so su dora mu a kan fahimtar nan ta Boko Haram da ISIS ta kin jinin wadanda ba Musulmi ba. Ba za mu amince da ita ba. Wannan shi ne abin da suke so.  So suke mu daina sallolinmu ne ko kuma mu daina mauludi ko kuma mu daina girmama Ranar Ashura? Tunda haka ne a bar su su kashe mu gaba daya,” inji shi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin