✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harbin kudan zuma ya kashe jami’in Kwastam a Legas

Rahotanni daga ofishin Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya wato (Kwastam), da ke iyakar Seme a Legas na cewa, babban jami’in hukumar mai suna Abba…

Rahotanni daga ofishin Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya wato (Kwastam), da ke iyakar Seme a Legas na cewa, babban jami’in hukumar mai suna Abba Abubakar ya rasa ransa  sanadiyyar harbin kudan zuma.

Abubakar Abba ya rasa ransa ne a lokacin da wani dandazon kudan zuma suka baibaye shi da harbi, a lokacin da jami’an ke sintiri a dajin Ashipa, kan iyakar Seme da ke yankin Badagry, a Legas.

Kakakin Jami’an Kwastan na Seme, Saidu Abdullahi, ne ya fitar da sanarwar cewa, lamarin ya faru ne a ranar Talatar da ta wuce, lokacin da Abba ke bakin aikin sa na sintiri a yankin.