Daily Trust Aminiya - Harin Boko Haram na Jakana ya jefa mutane cikin fargaba
Subscribe

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno

Harin Boko Haram na Jakana ya jefa mutane cikin fargaba

Da sanyin safiyar Litinin da ta gabata ce Boko Haram suka auka wa garin Jakana da ke kusa da garin Maiduguri, wanda hakan ya sa matafiyan da suka tashi daga Maiduguri zuwa jihohin Kano da Kaduna da Bauchi da sauransu suka shiga cikin halin kaka-ni- ka-yi. Sojoji sun rufe hanyar tun misalin karfe 9 na safe zuwa karfe 3 na yamma sakamakon harin.

Wakilinmu ya zanta da fasinjoji da direbobi da abin ya rutsa da su, inda  Abdullahi Jega da ke dauko jaridun Daily Trust daga Kano zuwa Maiduguri ya ce ya iso Jakana da misalin karfe 9 na safe, shigarsa ke da wuya ya fara jin harbe-harbe, amma Allah Ya tsallakar da shi. Ya ce ya ga an harbi wata motar Dangote.

Ahmed Mohammed wani direba da ya taso daga Bauchi, ya ce lamarin ya jefa mutane cikin fargaba da rudani,

Ya ce ya ga sojoji sun kama ’yan Boko Haram hudu sun daure su. Sai ya yi kira ga jami’an tsaro su kara kwazo, domin babu wata hanya a fadin Jihar Borno da aka fi zirga-zirga kamar wannan hanya, ga shi yanzu an fara jefa fargaba a zukatan matafiya.

Shi kuwa Ali Vectra ya ce faruwar lamarin ya sa su sun fara shakku kan cewa ana cin nasara a kan ’yan Boko Haram, “Domin idan ka duba hanyar nan ita ce kawai muke bi zuwa sauran jihohi da suka hada har zuwa Abuja da Legasda Kano da sauransu. To yanzu idan haka na faruwa, yaya za mu yi? Ba mu da wata sana’a in ba tuki ba,” inji shi.

Wani fasinja Ibrahim Muhammad ya ce sun ga tasku sosai, domin sun shafe awoyi da dama suna jira a cikin daji, Ya ce, “Muna jira wai Boko Haram sun kai hari, shin wane irin aiki sojoji suke yi? ”

Gwamnan Jihar Borno Farfersa Babagana Umara Zulum ya ziyarci kauyen na Jakana take bayan samu labarin kai harin inda a hanyarsa ta zuwa a daidai Jami’ar Jihar Borno ya tarar da daruruwan motoci, inda ake zargin jami’an tsaro suna karbar Naira 500 ko 1000 daga hannun matafiyan da ba su da katin dan kasa.Gwamnan ya nuna mutakar vacin rai kan haka, kuma ya bukaci hukumomin soja su dauki mataki a kai.

Wata mata mai suna Falmata Modu ta shaida wa Aminiya cewa hakika an nemi ta bada Naira 1000 saboda ba ta da katin shaidar dan kasa, a daidai wannan lokaci.

Direbobi da matafiya da dama sun zargi jami’an tsaro da tilasta su biyan kudi saboda rashin katin dan kasa a duk lokacin da za su shiga ko za su fita daga Maiduguri zuwa wasu yankuna.

texem
More Stories