✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin bom a masallacin idi ya hallaka gwamna a Afhganistan

Gwamnan gundumar Logar da ke kasar Afghanistan ya rasa ransa a wani harin bom da aka kai masallaci, lokacin da ake sallar idin layya. Arsala…

Gwamnan gundumar Logar da ke kasar Afghanistan ya rasa ransa a wani harin bom da aka kai masallaci, lokacin da ake sallar idin layya. Arsala Jamal yana tsaye a gaban masallacin idi, suna gaisawa da masu ibada, sai kawai wani bom da aka dana a karkashin tebur ya tashi da shi. A kalla mutum, 15 suka mutu a harin da aka kai Logar da ke Kudancin babban birnin kasar, Kabul, wato yankin da ’yan Taliban ke da karfin mulki.
Wannan harin da aka kai Logar an kai shi ne a babban masallacin kasar, a babban birnin gundumar da ke Pul-i-Alam, a cewar mai amgana da yawun hukuma, Din Mohammad Darwesh.
Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.
Marigayi Jamal ya karbi ragamar mulkin gundumar ne a watan Afrilun bana, bayan ya dawo Afghanistan daga kasar Kanada. A da shi gwamnan gundumar gabashin kasar ne, da ake kira Khost. Shi kwararre ne kan harkokin raya karkara, wanda ya yi aiki da kungiyoyin da ba ruwansu da gwamnati, kafin gwamnati ta ba shi mukami.
An kai wannan harin ne kwanaki kadan da rundunar sojan Amurka ta kama wani kwamandan ’yan Taliban na kasar Pakistan, Latif Mehsud, wanda aka ce na hannun damar Shugaban Taliban ne, Hakimullah Mehsud. Wakilin BBC Dabid Loyn da ke Kabul, ya bayyana cewa gundumar Wardak makwafciyar Logar sun zama wuraren da ba doka a tsawoncin shekaru.