✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harkoki sun koma yadda aka saba a Kurmi bayan kammala zabe

A Jihar Legas, cibiyar kasuwanci ta kasar nan al’amuran yau da kullum sun kankama bayan kammala zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa da…

A Jihar Legas, cibiyar kasuwanci ta kasar nan al’amuran yau da kullum sun kankama bayan kammala zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

A yankuna da dama na jihar da wakilin Aminiya ya kewaya lokacin zaben, an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da samun  tashin-tashina ba.  Yankunan  da wakilinmu ya kewaya sun hada da Unguwar Idi Araba da Apapa da Ajegunle da Ojota da Kasuwar Mil 12 da Agege, inda a rumfunan zabe da dama jami’an hukumar zaben suka fara aikin a kan lokaci sai dai akwai wasu wuraren da suka iso a makare,  kana a akasarin wuraren da wakilin namu ya zagaya, ba a samu matsalar na’urar zabe ba. Amma a yankin Okota da ke shiyyar Isolo an samu rahotannin hargitsi da tayar da husuma, inda wadansu matasa suka tarwatsa masu kada kuri’a a wasu rumfunan zabe; suka tarwatsa akwatunan zaben suka cinna wa kuri’un da jama’a suka kada wuta, lamarin da ya sanya wadansu matasa suka far wa mutumin da suka yi zargi da jan ragamar  yi musu satar akwatin zabe, inda nan take suka hallaka shi suka  kone shi da babur dinsa.

Wani abu da ya ja hankali a Jihar Legas a lokacin zaben shi ne karancin fitowar jama’a a lokacin zaben, duk da kasancewar jihar ita ce ta fi yawan wadanda suka karbi katin zabe da mutane sama da miliyan biyar, amma akasarin rumfunan zaben da wakilin Aminiya ya ziyarta an samu karancin fitowar jama’a; inda a wurare da dama ake samun kasa da sulusi ko rubu’in wadanda suka kada kuri’a, idan aka kwatanta su da yawan wadanda suka yi rajista.

Aminiya ta zanta da wani mai sanya ido a kan yadda zaben na Jihar Legas ya gudana, Malam Ahmad Yusuf wanda ya nuna gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da tsauraran matakan tsaro, inda ya ce ya zagaya sassan Legas da dama.

“A wasu wuraren an fara a kan lokaci misalin karfe takwas na safe, wasu wuraren an samu jinkiri, inda aka soma da misalin karfe 9 wani wajen 10; kai har akwai inda ba a fara ba sai karfe goma 11, amma alhamdulillahi, komai ya tafi daidai, an yi lafiya an kammala lafiya, wannan abu ya yi kyau kwarai,” inji shi.

Aminiya ta zanta da wadansu da suka kada kuri’unsu a daidai lokacin da ake ci gaba da dakon sakamakon zaben, inda a Kasuwar Mil 12 Alhaji Dauda Tarai, Shugaban ’Yan Tattasai na Kasuwar ya ce yanzu harkokin kasuwancin sun kankama gadan-gadan.

“Zan iya cewa ba a taba yin zabe cikin kyakkyawan tsari irin wannan ba, domin aikin ya tafi yadda ya kamata, inda a baya ake kawo na’urar zabe daya a yanzu biyu ake kawowa, sannan ma’aikatan sun nuna kwarewa a lokacin aikin zaben. Babu abin da za mu ce sai fatan Allah Ya sa nan gaba a dora a haka,” inji shi.

Hakazalika Alhaji Usman Shehu Samffan Sakataren Kudi na Kasuwar Mil12 kuma jigo daga cikin masu yakin neman zaben Shugaba Buhari a jihohin Kurmi, ya nuna gamsuwarsa da yadda zaben ya gudana.  “A yanzu jama’a da dama sun mai da hankalinsu a kan harkokin kasuwancinsu bayan mun fita mun sauke nauyin zaben Shugaba Muhammadu Buhari,” inji shi.

A daidai lokacin da wadansu ke ta murna samun damar kada kuri’arsu, wadansu kuwa sun ziyarci rumfar zabe tare da katin zabensu amma ba su samu ikon kada kuri’a ba.

Aminiya ta ci karo da wata mata a rumfar zaben Barikin Sojin Ruwa da ke daura da Mobil a Apapa. Matar da ta yi ta sharbar kuka domin ba ta samu damar zaben Shugaba Buhari ba.  Ta shaida wa Aminiya cewa sau uku tana hawa layin zaben amma na’urar zaben ba ta karbi katin zabenta ba. “Ina cikin bakin cikin ganin yadda na’urar ta ki karbar katin zabena, ta hana ni damar zaben wanda na dade ina fata in zaba,” ta fadi haka cikin kuka.

Hakazalika Aminiya ta ci karo da wani mutum mai suna Muhammad a Idi Araba, wanda shi ma ya gaza kada kuri’arsa saboda ya kasa gano rumfar zaben da ya kamata ya kada kuri’a. “Tun bayan Sallar Asuba na fito domin in kada kuri’a a wannan mazaba ta Gidan Sarki na yi rijista amma na je sun ce babu sunana a wajen. Zuwa yanzu na karade daukacin rumfunan zaben wannan unguwa amma ban ga sunana ba, wannan abu ya tayar min da hankali kwarai” inji shi.

Aminiya ta ga wadansu mutane da suka yi cirko-cirko a gefen rumfunan zaben amma ba su da katin kada kuri’a, lamarin da ya sanya su komawa baya inda suka zauna suka zama ’yan kallo. Wadansu daga cikinsu sun ce sun yi rajistar katin zabensu a jihohinsu na Arewa ne kuma rashin kudi ya hana su tafiya can su kada kuri’a.

Malam Abubakar wanda mutumin Jihar Neja ne da bai samu damar kada kuri’arsa ba, ya shaida wa Aminiya cewa a wanccan makon da aka shirya yin zaben, ya shirya tsaf inda ya tafi garinsu da zimmar kada kuri’arsa ga Shugaba Buhari, “Amma dage zaben da aka yi ne ya sanya na rasa kada kuri’ar, domin ni a nan Legas nake neman abincina. Koda na je gida da niyyar yin zabe aka kuma dage sai na dawo ranar Laraba domin ba zan iya ci gaba da jira ba, a nan nake neman abinci,  amma har gobe wanda nake kaunar kada wa kuri’ata wato Shugaba Buhari yana raina” inji shi.