✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harkokin noma sun habbaka sakamakon samar da kamfanin Olan – Abdul’azeez Gidan dutse

Wani babban manomi da ke zaune a kauyen Gidan dutse da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, Alhaji Abdul’azeez Yakubu Gidan Dutse ya bayyana…

Wani babban manomi da ke zaune a kauyen Gidan dutse da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, Alhaji Abdul’azeez Yakubu Gidan Dutse ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya taimaka wa manoman Jihar Kaduna da sauran manoman da suke makwabtaka da Jihar, sakamakon kawo kamfanin sarrafa kayayyakin amfanin gona na Olan zuwa jihar.

Alhaji Abdul’azeez Gidan Dutse ya bayyana hakan ne, lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya.

Ya ce, duk manomin da ya ce, baya son gwamna El-Rufa’i bai yi daidai ba, domin ya kawo wa manoma kamfanin sarrafa amfanin gona na Olan a Kaduna.

Ya ce, ada sai manoman Jihar Kaduna sun kai masarar da suka noma Fatakwal ko Legas ko yankin Inyamurai. Ya ce, amma yanzu a Jihar Kaduna sakamakon zuwan wannan kamfani na Olan, manoman sukan kai masarar da suka noma su  sayarwa wannan kamfanin, ba tare da wata matsala ba.

Ya ce bayan haka, Gwamna El-Rufa’i ya gayyato babban dan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote zuwa Jihar Kaduna, ya ce nan gaba zai kaddamar da kamfanin fulawa a Jihar.

Ya ce, wannan ba karamin taimakawa manoman zai yi ba, domin duk kayayyakin amfanin gonar da manoma zasu noma, idan babu mai saye sun yi aikin banza.

Alhaji Abdul’azeez ya yi bayanin cewa ya fara noman masara  tun a shekara ta 1982,  lokacin da tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ya kawo  masara Najeriya. Ya ce, shi ne ya fara karbar noman masara a yankin Karamar Hukumar Lere ta jihar Kaduna.