Search
Subscribe
Hassada ga mai rabo taki ne

Hassada ga mai rabo taki ne

Assalamu alaikum Manyan Gobe.  Da fatan kuna cikin koshin lafiya.  A yau ga wani labari na kawo muku mai taken “Hassada ga mai rabo taki ne.” Da fatan Manyan Gobe za ku dauki darasi daga wannan labari.

A garin Maidaki an yi wani magidanci mawadaci. Wannan maigida ya kasance yana da mata hudu. Sai dai duk a cikin matan ya fi son amaryar wadda ake kira Mairo saboda biyayya da take yi masa.

Sana’ar wannan maigida ita ce fatauci inda yakan shafe tsawon lokaci ba ya gida. A duk lokacin da zai yi tafiya yakan tara dukkan matansa ya tambaye su abin da zai sayo musu idan zai dawo. Kowacce takan fadi abin da take so amma ban da Mairo.

A kowane lokaci ya tambayi Mairo abin da zai saya mata sai ta amsa masa da cewa duk abin da ya ga ya yi masa yake kuma da halin saye.

Ashe wannan abu da Mairon take yi yana bata wa sauran matan gidan rai inda suke ganin abin da take yi a matsayin kissa da kisisina don haka suka dauki aniyar ganin sun yi abin da za su yi wanda zai sa ta bar gidan gaba daya.

Za mu ci gaba

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin