✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hauma-haumar haramar handama

Dagwalon dagula Dillalan dillancin dila Dandalin dafdala Dalilin daudar dala Dungulmin dandamalin damalmala   ’Yan jam’iyyu An ci gayu An yi taron yuyu Ana ta…

Dagwalon dagula

Dillalan dillancin dila

Dandalin dafdala

Dalilin daudar dala

Dungulmin dandamalin damalmala

 

’Yan jam’iyyu

An ci gayu

An yi taron yuyu

Ana ta dabi’ar mayu

Kuri’un talaka sun zam layu

 

Kugiyar kirgar kato

Karatan kwafta kofato

Kundumbalar runto

Kusumbin kobobo

Kabar kwambon rahoto

 

Koto

Karfa-karfan kato

Kolon kulunboto

Kifadin masu kwarmato

Karajin kwafta kofato

 

Laulauyin layi dogo

Tsayi iwa tarago

Duk mai karfi ya na shago

Lokaccin wulwulawar agogo

Taka-kara aka kago

 

An karya wa al’umma lago

Wakili na jira a kango

Damin kudi aka kirgo

An jinka wka gwaggo

’Yan jagaliya an tattaro

 

Masu lullubin bargo

Kumbiya-kumbiyarsu an hango

Tsakar dakinku aka shigo

An ga na kuryar kogo

Yana can makalkale a bango

 

Fafutikar fitar da gwani

Wasu sun yi gwangw2ani

Suna ta yi wa juna gunguni

’Yan daba a sansani

Aika-aikar rashin sani

 

Tsiwar tsintsiya

Tsirar tsere tsara da tsiya

Tsayuwar tsaiwa

Tsawar tsiwa

Tsarin tsamoin tsamiya

 

Lallai Baba a gyara

Babu abin da ya gagara

Mai-duka ya ba mu nasara

Hankula su tattara

Mu daina kwabar tabara

 

Masu carar zakara

Karairayi suka kirkira

Dukiy suke son gurgura

Wuyan talaka ya sha makara

Tattalin tafka asara

 

A hana almajirai bara

Gajiwar talaka ce raguwar dabara

’Ya’ya su daina yawo tsirara

Makiran miyagu na sa mura

Mu dai daura dammara

 

Danboto an saya

Tuni an biya

Wakilan danniya

Wawurar waskiya

Wautar watangaririya

 

Teren taraliya

Taune-taunen cin taliya

Tattakin tutiya

Tufafin tunfafiya

Talalar tunkiya

 

Harigido da Hatsaniya

Hayagagar hayaniya

Has ashen hanya

Hautsinin hikaya

Haka-haka ake ta kaya-kayya

 

Kanen Baba-Ojo

Zai taka rawar banjo

Kasar ya cefanar a gwanjo

A tara kudin ajo

Don cutar da su Hajo

 

Tulun tumbin wulli

Tufka da warwarar asali

Tabarar rashin hankali

Tururuwar fantamawar fatali

Taron ga na da jan hankali

 

Tambelen tumbin wulli

Turakun tunkude tubali

Tarwatsa tarin tattali

Tambada tuli-tuli

Tambotsan tankwali

 

Rarumar rikon ragama

Rummacen romon rigima

Ruwan randa daga korama

Rangajin rikon rakuma

Rakashewar rudu an runtuma

 

Saurayin kirinki

Suinkurun rashin kirki

Sasarin shaken shan buki

Sakarcin surkuki

Suburbudar sakarai a daki

 

Haurobiyawa barka da warhaka, hakika an TSUWURWURTA TSIYA-TSIYA A TSARIN TSAYUWAR TSAIWAR TSAWAR TSINTSIYA, amma duk da haka fafutikar fitar da gwanin al’umma na jam’iyyar tsintsiya ya zarta na mai dan boto tsabta. Domin sanin kowa ne a kasar nan cewa TSOHON KANEN BABA-OJO, mai gonakin Otawa shi ya ciri tuta bayan da ya TSUWURWURTA DABDALAR DALA A DANDAMALIN DAMALMALA. Sannan an yi TAMBELEN TUMBIN-WULLI DA SASARIN SUNKURUN SAURAYIN-KIRINKI a gaban FATALWAL-KWAL. Fatanmu dai kada a damalmala mana kasa.

Haurobiyawa dai ’yan takara da masu taka kara sun yi wa wuyahnku makura, domin lallai ya kamata mu fasko cewa an kassara DAMA-DAMA-DA-KURDA-KURDAR WASAN SAMSON-SIYA-SIYA a siyasar kasar nan, tunda dai ana nan a turbar tsarin DAMO-DA-KURA-DA-DIYYA.

Lallai mu yi wa kawunanmu kiyamullaili, mu yi kokarin tantance kimar darajar wadanda ya kamata su  yi WAKILCI DA JAGORANCI a tsakanin al’umma, musamman a wannan lokaci da bara-gurbi suka yi dandazon kwasar gararumar jar-miyya. To kafin su yi mana mamaya, wajibi ne a TANTANCE TSAKUWA DA TSABA. Ka da mu bari a koma gidan jiya, ballantana kasarmu ta karke da jinya.

’Yan makaranta masu koyon watsattsake da falle shafukan wagagen littattafai da mujallu da makalu, har ma da baza na zomo a akwatunan bututun batutuwa da baje na-mujiya a gaban akwakun wulkitawar hotuna, lokaci ya yi da za mu rika bin manhaja mara hajijiya a wajen gudanar da harkokin kasar nan.

Zabi-sonka da ke karatowa na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama, ya kamata kowa ya bayar da gudunmuwarsa wajen canko mana managartan wakilai da jagororin al’umma, wadanda za su bayar da himma, ba tare da hauma-hauma ba, ballantana su kyale jama’a su yi ta hamma.

Lallai an tafka kura-kurai a daukacin jam’iyyu kasar na, don haka muke kira ga Gwamnatin Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajon Haurobiya kan lallai a yi mai yiwuwa wajen aiwatar da gyare-gyare., amma ba ’YAN GYARE-GYARE IRIN NA-GYARE DA KUREGE BA. Kowa ya sani mugun aikin da su Baudadden Jojin Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge suka tafka ya sanya Marigayi Shugaba ‘’Yarbishiya ya sanya aka yi aikin gyara fasalin zabi-sonka a kasar nan. Da baban Baba zai yi kokarin kara fito da managarcin tsari. A halin yanzu dai kowa ya san yadda ake ta HAUMA-HAUMAR HARAMAR HANDAMA, wato akwai miyagun da ke a bar su su dama, su yi rawar gaban hantsi, alhali jama’a na tsi-tsi!

Ba tare da na cika ku da surutu rututu ba, kamar kamfanin dillancin labarai na Reuters, sai in ce mu yi ta fatan ganin an gudanar da wannan zabi-sonka da ke karatowa cikin LULLUMIN LUMANA LULLUM!