✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausawa da Fulanin Abuja sun jaddada goyon bayansu ga Shugaba Buhari

Kungiyar Al’ummar Hausawa da Fulani ta Abuja ta jaddada goyon bayanta ga Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari inda ta sha alwashin…

Kungiyar Al’ummar Hausawa da Fulani ta Abuja ta jaddada goyon bayanta ga Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari inda ta sha alwashin fadakar da al’ummarta kan yadda za su ci gajiyar manufofin gwamnatin na taimaka wa al’umma.

Jagoran kungiyar na yankin Birnin Tarayya, Alhaji Yakubu Sa’idu ne ya bayyana haka yayin taronsu na Bikin Sallah da ya gudana a garin Gwagwalada, Abuja.

Alhaji Yakubu ya ce,  Gwamnatin Buhari ta tsara manufofi na inganta rayuwar al’umma da sauran jama’a daga wasu wurare ke amfana a kai, saboda haka ya ja hankalin ’yan kungiyar su bai wa lamarin goyon baya wajen shiga a dama da su tare da bin ka’idoji kamar wajen aiwatarwa da kuma mayar da bashi da ake rantawa don inganta sana’a, a kan lokaci.

Haka nan ya ce kungiyar wadda aka kafa bara, tana shirin kafa wata gidauniya don taimaka wa masu rauni a cikin al’umma a fuskar neman ilimi da sana’a da kuma kiwon lafiya.

Sarkin Hausawan Idu-Abuja Malam Muhammad Zakari, ya yaba da tsarin zaman lafiya a tsakanin al’ummar inda ya ce ci gaba ko tallafin gwamnati ba zai samu ba sai da haka.

A jawabinsa a madadin al’ummar Fulanin Abuja, wani jagoran matasan Fulani daga Gwgwalada, Malam Mahmud Ibrahim Ingale ya ce al’ummarsu musamman makiyaya na baya ga dangi wajen cin gajiyar harkokin gwamnati a fuskar karatun zamani da sauran abubuwan more rayuwa. Ya ce saboda haka ya ji dadi da kungiyar ta ce za ta kirkiro hanyoyi da za ta taimaki sha’anin karatu da sauran al’amura na mambobinta.