✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausawan Legas sun roki shugabannin Arewa su tsoma baki kan matsalarsu

Sarkin Hausawan Idimu da ke yankin Alimosho a Jihar Legas Alhaji Bello Musa ya bukaci gwamnoni da shugabannin Arewa su taimaka wa Hausawa mazauna Legas…

Sarkin Hausawan Idimu da ke yankin Alimosho a Jihar Legas Alhaji Bello Musa ya bukaci gwamnoni da shugabannin Arewa su taimaka wa Hausawa mazauna Legas game da matsalar matsuguni da suke fuskanta. Sarkin ya ce, “Duk da yake yanzu ana samun kyakkyawar zamantakewa tsakanin Yarbawan Legas da Hausawa, matsalar matsuguni ta addabi Hausawan inda ake samun akalla fiye da mutum 100 suna zaune a rumfa daya. Wannan ne ya sa muke kira ga sarakuna da dattawa da tsofaffin shugabannin kasa da gwamnonin da suka fito daga Arewa su taimaka su kawo mana dauki a kan wannan matsala.”                                                                                                                                              Sarkin Hausawan ya yi kiran ne a zantawa da Aminiya a ofishinsa da ke hanyar Asumbe a Legas. Ya ce “Mafi yawancinmu da muke zaune a Legas muna yin ayyukan karfi ne da suka hada da leburanci kamar hakar shadda da rijiya da sana’ar acaba da fawa da gadi sai masu kananan shaguna, saboda haka a matsayinmu na wakilan sarakunan Arewa a nan nake neman alfarmarsu su mika kokenmu ga duk wanda alhakin magance matsala ke wuyansa a taimaka wajen fitar damu daga cikin wannan kuncin rayuwa.”

Sarkin Hausawan ya ce “Muhimmin abin da muke rokon shugabannin Arewa su kawo mana dauki a kai su ne  bayar da tallafi domin sama mana matsunguni na dindindin a Legas ba irin yadda muke zaune a warwatse yanzu cikin wannan gari inda hakan ke taimakawa wajen samun sabani a tsakanin mutanenmu da jama’ar gari. Kuma muna rokon shugabannin Arewa su yi duk abin da suke iyawa wajen ganin masarautu da gwamnatoci a Kudu sun fara biyan albashi ko alawus ga sarakunan Hausawa kamar yadda Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi ya fara sanya sarakunan kabilun Ibo da Yarbawa a cikin  hakimai a masarautarsa.”

Dangane da zamantakewarsu da sauran jama’a, Alhaji Bello Musa ya ce “A gaskiya ta wannan fanni sai godiya domin muna yin taron Sarakunan Hausawa na Karamar Hukumar Alimosho a karkashin shugabancin Alhaji Ahmed Haruna Kuraje, inda muke duba matsalar rashin jituwa a tsakanin Yarabawa da Hausawa da sauran matsaloli.

Yanzu an samu saukin irin wadannan matsaloli domin a kowane lokaci aka samu aukuwar haka su da kansu shugabannin Yarbawan ne suke kawo mana Bahaushen da suke zargi domin daukar mataki. Haka mu ma muke yi, sabanin shekarun baya da ake kaurewa da fada a tsakanin kabilun biyu.”