✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Henry ya zama kocin Monreal Impact na Amurka

Tsohon Kyaftin din kulob din Arsenal da ke Ingila Thierry Henry ya zama kocin kulob din Monreal Impact da ke Amurka.  Henry ne da kansa…

Tsohon Kyaftin din kulob din Arsenal da ke Ingila Thierry Henry ya zama kocin kulob din Monreal Impact da ke Amurka.  Henry ne da kansa ya sanar da haka a shafin sadarwarsa na Twitter a ranar Asabar. Ya ce ya sanya hannu ne a kwantaragin shekara 2 da zimmar idan ya yi kokari za a iya kara masa wa’adin shekara 1.

Wannan shi ne karo na farko tun a watan Janairun bana da Henry ya sake samun aikin horarwa. A watan Janairun bana ne kulob din Monaco na Faransa ya kori Thierry Henry saboda rashin kokari.

Thierry Henry dai ya taba yin kwallo a kulob-kulob da dama da suka hada da Monaco na Faransa da FC Barcelona na Spain da Arsenal na Ingila da New York Red Bull na Amurka kafin ya zama koci.