✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar DSS ta wanke mutum 21 da zasu samu mukaman ministoci

Kimanin sunayen wadanda ake saran bai wa mukaman ministoci 21 ne, Hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta wanke; a daidai lokacin da ita kuma…

Kimanin sunayen wadanda ake saran bai wa mukaman ministoci 21 ne, Hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta wanke; a daidai lokacin da ita kuma majalisar dokokin Najeriyar ke komawa bakin aiki daga wani dogon hutun ta shiga a yau Talata. Kamar dai yadda majiyoyi da dama suka tabbatar wa Aminiya.

Aminiya ta kuma fahimci cewar, bayan tantancewar, Hukumar SSS din za ta mika sunayen ne ga zauren majalisar dattijai ta kasa, dan neman mincewarsu a kai, kamar dai yadda kundin tsarin mulki na shekarar 1999 ya tanadar.

An sha ruwaito fadar Shugaban Kasa ta na mai bayar da tabbaci ga ‘yan Najeriya cewar, a wannan karon ba za a share tsawon lokaci ana jiranta da ta kafa majalisar ministoci ba.

Idan dai za a iya tunawa, a shekarar 2015, Shugaba Buharin ya yi ta jan kafa har na tsawon wata shida gabanin ya mika sunayen wadanda yake son ya nada ministocinsa ga zauren Majalisar Dattawan.

Aminiya ta fahimci cewar, daga cikin wadanda aka tantancen, da akwai wasu tsoffin ministocin gwamnatin Buharin. Biyu daga cikin hadiman tsoffin ministocin sun ce masu gidan nasu sun tabbatar musu cewa lallai an tantance su.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 28 ga watan Mayu, Shugaba Buhari ya rushe majalisar Ministocin nasa; sai dai jiga-jigan majalisar irin su Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mustapha Boss da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari da dai sauransu da dama, sun ci gaba da rike mukaman nasu, ba tare da an sake sabunta su ba.