✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar EFCC ta gayyaci Sanata Bukola Saraki

Hukumar Yaki da Almundahana da yi wa Tattalin Arziki Zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kwara, Sanata Bukola Saraki a gabanta inda…

Sanata Bukola Saraki, tsohon gwamnan Jihar KwaraHukumar Yaki da Almundahana da yi wa Tattalin Arziki Zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kwara, Sanata Bukola Saraki a gabanta inda ta yi masa wadansu tambayoyi dangane da zargin yin sama-da-fadi.
Sanata Saraki, wanda shi ne shugaban kwamitin kare muhalli a majalisar dattijai, ya isa farfajiyar hukumar ne ranar Litinin da safe don amsa gayyatar da ta yi masa tun wadansu makonni da suka gabata.
Aminiya ta kalato cewa ana bincikensa ne saboda wata badakalar kudi da aka yi a lokacin da yake gwamna.  Ya ci zaben zama gwamna ne a shekarar 2003 sannan ya sake hayewa a zaben shekarar 2007.  A shekarar 2011 ce ya zama sanata, bayan da ya kammala shekaru takwas a kan kujerar gwamna.
Abin da ake zargin nasa a kansa dai bai fito fili ba, amma ana tsammanin binciken nasa zai hada da tun lokacin da yake matsayin daraktan gudanarwa a bankin Societe Generale na Najeriya (SGBN).
Lokacin da aka tuntubi kakakin hukumar EFCC, Mista Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa hukumar ta turke sanata Saraki, inda ta yi masa tambayoyi.
A daren Talata jami’in hulda da manema labarai na Sanata Saraki, Mista Bamikole Omishore ya fitar da wani gajeren bayanin cewa sanatan, “Ya dawo gida, bayan da ya karba kiran da hukumar EFCC ta yi masa, kamar yadda ya yi alkawari idan ya komo daga Umara.  Ma’aikatan hukumar dai sun nuna halin dattaku da iya aiki a lokacin da suke yi wa Sanata tambayoyi, kuma tuni ya koma gida”. Inji shi.