✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar EFCC ta gurfanar da Maman Boko Haram kan cin amana

Hukumar  Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gurfanar da A’isha Wakili wadda aka fi sani da Maman Boko Haram da wasu mutum…

Hukumar  Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gurfanar da A’isha Wakili wadda aka fi sani da Maman Boko Haram da wasu mutum biyu a gaban Babbar Kotun Maiduguri, bisa zarginsu da zamba cikin aminci.

Maman Boko Haram tana shugabantar wata kungiya mai zaman kanta, mai suna Complete Care and Aid Foundation. Sauran mutum biyun sun hada da Tahiru Alhaji Sa’idu Daura da kuma Lawal Shoyade, wadanda suke rike da mukaman Manajan Shirye-Shirye da kuma Daraktan Cibiyar ta Kasa.

Da yake gabatar da wadanda ake zargi a gaban Mai shari’a A’isha Kumalia, mai gabatar da kara Benjamin Manji ya shaida wa kotun cewa mutum ukun da wani Sa’idu Muktar da ya tsere, a wani lokaci a tsakanin watan Yuni zuwa Agusta 2018, sun gabatar da takardun karya kan su karbi kudade wanda yin hakan ya saba wa sashi na 8 na dokokin manyan laifuffuka.

Ya ce sun karbi Naira miliyan 45 daga hannun Mohammed Umar Mohammed na Kamfanin Nyeuro International kan yin wata kwangila ta sayo kayan abinci na karya.

Dukkan wadanda ake zargin sun musanta zargin da ake musu, inda Mai shari’a A’isha Kumalia ta dage sauraren karar zuwa 10 ga watan gobe, domin ci gaba da shara’ar.