✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar EFCC ta yi wa Karamar Hukumar Zariya dirar mikiya

A shekaranjiy Laraba ce jami’an Hukumar EFCC suka yi wa Karamar Hukumar Zariya dirar mikiya. Wata majiya ta shaida wa  Aminiya cewa zuwan jami’an Hukumar EFCC…

A shekaranjiy Laraba ce jami’an Hukumar EFCC suka yi wa Karamar Hukumar Zariya dirar mikiya.

Wata majiya ta shaida wa  Aminiya cewa zuwan jami’an Hukumar EFCC karamar hukumar ta  biyo bayan wasu korafe-korafe ne da aka kai wa hukumar kan yadda ake tafiyar da kwangiloli a karamar hukumar.

Kafin zuwan jami’an EFCC wata majiya ta ce kwanakin baya, ta gayyaci Shugaban Karamar Hukumar da wadansu ma’aikatansa kan takardar korafin da ta samu daga wadansu mutane.

Sai dai a wancan lokaci takardar korafin ta kasance na jeka-na-yi-ka na ne saboda babu cikakken suna da adireshin wanda ya rubuta takardar.

A watannin baya, Karamar Hukumar Zariya ta fitar da kwangiloli na sama da Naira miliyan dubu daya.

Zuwar Hukumar EFCC karamar hukumar ya jefa jami’an karamar hukumar cikin dimuwa.

Bayanan da Aminiya ta samu sun ce Kansilan Ayyuka na Karamar Hukumar Zariya ya yanke jiki ya fadi lokacin da jami’an EFCC suka bukaci duk wanda ke da alaka da gudanar da ayyuka ya gurfana a gabansu, kuma Kansilan Ayyukan yana cikin wadanda ake zargin da kasancewa dan gaban goshin Shugaban Karamar Hukumar da duk kwangilar da za a bayar da masaniyarsa.

Kafin zuwan EFCC sai da wani ayarin masu bincike daga Hukumar Kula da Kananan Hukumomi ta Jihar Kaduna ya kwashe mako daya yana gudanar da bincike a karamar hukumar.

Da Aminiya ta nemi jin ta bakin Shugaban Karamar Hukumar Injiniya Aliyu Idris Ibrahim ta wayar hannu sai ya ce, “Ita hukumar ce ta fada maka ko kuma wani ne ya fada maka? Don haka ni ban sani ba, amma ka je ka rubuta abin da aka fada maka.”