✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar FIRS ta karbo harajin Naira biliyan 13 daga attajirai

Hukumar Tara Haraji ta kasa, (FIRS) ta ce ta samu nasarar karbo harajin Naira Biliyan 12.66 daga hannun attajiran kasar nan a cikin wata daya.…

Hukumar Tara Haraji ta kasa, (FIRS) ta ce ta samu nasarar karbo harajin Naira Biliyan 12.66 daga hannun attajiran kasar nan a cikin wata daya. Shugaban Hukumar, Tunde Fowler ne ya sanar da haka lokacin da ya karbi bakuncin Ministar Kudi, Hajiya Zainab Ahmed a ranar Juma’ar da ta gaba.

Mista Fowler ya shaida wa Ministar cewa, a karkashin shirin nan na bibiyar asusun ajiyar attajirai da ke bankunan kasar nan, an samu nasarar tura kimanin Naira biliyan 12 da miliyan 66 ga asusun Gwamnatin Tarayya. Ya ce, hukumar ta rubuta wa dukan bankunan kasuwanci wasiku a cikin watan Mayun bana, don neman sunayen kamfanoni da ’yan kasuwa da kuma na masu yin kasuwancin hadaka da suka mallaki Naira biliyan daya zuwa sama.

Ya ce, an yi hakan ne don a tantance kamfanonin da suke bin dokar biyan haraji da wadanda ba sa bin dokar, inda kawo yanzu, wadanda ba sa bin dokar, an samu nasarar karbo harajin da ya kai Naira biliyan 12 da miliyan 660. Shugaban ya ce, hukumar za ta ci gaba da aiwatar da shirin don ganin ana bin dokar biyan harajin don samar wa gwamnati kudin shiga da kuma ci gaba da wayar da kai da kuma wanzar da biyan harajin BAT a sauran fannonin tattalin arzikin kasa da samar hanya mafi sauki ta biyan harajin, musamman ga kananan masu biyan harajin da karfafa karbar haraji ta yin hadin gwiwa da hukumomi kamar na hukumar tara harajin.

A jawabin Ministar ta yaba wa hukumar a kan tara kudin harajin, inda ta ce, ma’aikatar ta za ta ci gaba da hada hannu da hukumar don ba ta dukan goyon bayan da ya dace a kan karbo wa gwamnatin haraji, za ta kuma rika tuntubar hukumar a koyaushe. “A gare mu, umarnin da aka ba ni shi ne in kara habaka samar da haraji ga gwamnati kuma aiki ne mai muhimmanci a gabanmu kwarai, ina jinjina muku bisa wannan kokari kuma sakamakon aiki shi ne, a kara ba da himma kada ku gajiya ganin cewa kasar ta dogara ne a kan hukumar wajen kara tara haraji don tallafa wa gwamnati,”  inji ta.

Hajiya Zainab ta yi kira ga hukumomi su yi aiki kafada-da -kafada wajen ganowa da bankado masu cin hanci da rasshawa a kasar nan, inda ta ce, wannan umarni ne daga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Ta yi nuni da cewa, hukumar tana da muhimmanci a wajen gwamnati inda ta ce saboda muhimmanci da take da shi ne ya sanya wannan ziyararta ta farko zuwa don fara ganawa da ita.

Ministar ta ce, kasar nan tana bukatar a rika tara haraji ba lallai ta hanyar dogaro a kan man fetir ba, har da fannin da bai shafi mai ba, kuma abin da ake bukata shi ne, hukumar ta ci gaba da kokarin da take yi na tara haraji ba ta hanyar mai kadai ba.