✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar NAFDAC ta gargadi masu sayar da shayi

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), ta gargadi ’yan Najeriya a kan su yi taka-tsantsan wajen shan shayi a bakin titunan…

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), ta gargadi ’yan Najeriya a kan su yi taka-tsantsan wajen shan shayi a bakin titunan birane da garuruwan kasar nan, bisa zargin da ake yi cewa, wadansu daga cikin masu sayar da shayin na sanya wasu sinadarai da ka iya zama hadari ga lafiyar dan Adam.

Sayar da shayi na daya daga cikin kananan harkokin kasuwanci masu dogon tarihi da suka dade suna bada gudunmawa ga habbakar tattalin arzikin iyalai a Afirka ta Yamma kamar Najeriya da Nijar da makamantansu.

Wannan gargadi na kunshe ne a wani rahoto da Muryar Amurka ta wallafa a shafinta na Intanet.

Kamar sauran birane da kauyuka a yankin Afirka ta Yamma, harkar sayar da  shayi na daga cikin hanyoyin samun abinci ga mabukata cikin sauki da sauri a Kano da sauran sassan Najeriya.

Baya ga haka, sayar da shayi na cikin jerin kananan harkokin kasuwanci da ke samar da kudaden bukatun yau da kullum ga dimbin masu wannan harka a karkara da birane.

Sai dai an dade ana zargin wadansu daga cikin masu sarrafa shayi kan suna sanya wasu sinadarai a cikinsa, wa lau na itatuwa ko wadanda Bature ya sarrafa da ka iya zama illa ga dan Adam.

Rahoton ya ce ta yiwu hakan ya sa Hukumar NAFDAC ta gargadi ’yan Najeriya kan su yi suyi taka-tsantsan da masu sayar da shayi a bakin titi.

To amma Malam Nura Iliyasu, wani matashi da ya shafe fiye da shekara 15 yana  sayar da shayi daura da Sinimar Plaza a Unguwar Fagge a birnin Kano ya ce duk kayayyakin shayin da suke amfani da su wadanda hukuma ta amince da su ne.

Dokta Usman Mohammed na Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, ya ce batun tsabta shi ne babban abin da hukumomi ya kamata su bada himma sosai a kan duk wani nau’in abinci da ’yan kasa ke ci.

Malam Nura Iliyasu ya ce, daga cikin masu sarrafa shayi, akwai masu hade-haden itatuwa ko sinadarai da sunan kara wa mutum kuzari, koda yake ya ce ba ya da cikakkiyar masaniya game da sigar da suke bi wajen hada irin wannan shayi.

Ita kuwa Hukumar NDLEA mai yaki da ababen sanya maye da aka tambaye ta kan ko tana da rawar takawa a kan mutanen da ke hada irin wannan shayi su sayar wa Jama’a? Dokta Ibrahim Abdul, shi ne Kwamandan Hukumar a Jihar Kano, ya ce suna iya yin amfani da sashe na 20 da 19 na dokarsu da ta ce duk wanda aka kama yana hada kayan maye, za a iya gurfanar da shi ko ita a gaban kotu.

Sai  dai Dokta Usman ya ce akwai bukatar Hukumar NAFDAC ta gudanar da sahihin bincike ta sigar ilimin kimiyya game da wannan batu, domin kauce wa yanayi na yi wa masu harkar shayi kudin goro.

Batun kiyaye tsabtar abinci da daidaikun nau’o’in cimaka da jikin dan Adam ke bukata shi ne babban ginshikin gina al’umma mai cike da koshin lafiya, kuma nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati da al’umar kasa, kamar yadda masana suka sha nanatawa.