✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukuncin kotu: ’Yan majalisa 37 da suka koma APC za su daukaka kara

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa ’yan Majalisar Wakilai 37 da suka bar PDP zuwa Jam’iyyar APC, su sauka daga…

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa ’yan Majalisar Wakilai 37 da suka bar PDP zuwa Jam’iyyar APC, su sauka daga kujerunsu na majalisar.
Da yake yanke hukunci kan karar da Jam’iyyar PDP ta shigar tana neman a hana ’yan majalisar sauya shugabannin majalisar, Alkalin Kotun Mai shari’a Adeniyi Ademola ya ce ’yan majalisar su ajiye mukamansu saboda sauya sheka daga jam’iyyar da aka zabe su alhali wa’adinsu bai kare ba.
A watan Janairu ne Jam’iyyar PDP ta shigar kara tana neman a hana wakilan majalisar sauya shugabanninta, kuma ta shigar da karar ce bayan sauya shekar wakilan 37 a ran 18 ga Disamban bara.
A cewar kotun daga yanzu, ’yan majalisar ba su da ikon tafka muhawara a kan abubuwan da ke gudana a zauren majalisar. Kuma alkalin ya haramta wa ’yan majalisar da suka canja shekar sauya shugabannin majalisar.
’Yan majalisar da hukuncin ya shafa sun hada da Nasiru Sule Garo da Ahamd Zarewa da Sani Aliyu Madaki da Bashir Baballe da Alhassan Ado Doguwa da Mannir Babban dan-Agundi da Aminu Sulaiman Goro da Abdulmmumin Jibrin da Musa Ado Gezawa da Mustapha Bala Dawaki da Muhktar Chiroma dukkansu daga Jihar Kano.
Sauran sun hada da wakilan da suka fito daga Jihar Sakkwato da suka hada da Kabiru Marafa Achida da Aminu Shagari da Isa Salihu Bashir da Abdullahi Mohammed Wammako da Sa’adu Nabunkari da Aliyu Shehu da Shu’aibu Gobir da Musa Sarkin Adar da Abdullahi Balarabe Salake da kuma Umar Bature, wanda a watan Janairu ya sake komawa PDP.
Wadanda suka canja sheka daga Jihra Ribas sun hada da Andrew Uchendu da Asita Honourable da Sokonte Dabies da Dakuku Peterside da Mpigi Barinada da Pronen Maurice da Dawari George da kuma Ogbonna Nwuke.
Sai Ali Ahmad da Rafi’u Ibrahim da Aiyedun Akeem da Mustapha Moshood da Ahman Patigi da  Zakari Mohammed daga Jihar Kwara, sai kuma Yakubu Dogara daga Bauchi da Nasiru Sani Zangon Daura  daga Katsina. Tuni ’yan majalisar da abin ya shafa suka ce za su kalubalanci hukuncin a Kotun daukaka kara.
Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Mista Femi Gbajabiamila ya yi fatali da hukuncin inda ya bayyana shi da bakon hukunci da aka murguda shari’a. Shi kuwa Aliyu Sani Madaki na APC daga Kano cewa ya yi an yanke hukuncin ne da muguwar manufa domin zubar da mutuncin bangaren shari’a. “Wannan hukunci ne na kasuwar bayan fage da ba za a samu irinsa ba a ko’ina. Hakika ya zubar da mutuncin bangaren shari’a… Baya ga haka alkalin kotun ya fice daga bukatun da aka gabatar masa, wanda ya nuna shari’ar kasuwar bayan fage ne domin ya dadada wa PDP… kuma za mu daukaka kara a kai,” inji shi.
Shi lauyan ’yan majalisar 37 Mahmud Abubakar ya shaida wa wakilimu ta waya cewa alkalin “ya fada cikin wani lamari da ba a nema a cikin karar ba.”
Sai dai mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar Leo Ogor ya bukaci ’yan majlaisar 37 cewa kada su bata lokacinsu wajen daukaka kara tunda sun riga sun fadi a tashin farko.