Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Idan Ibo suka ki yarda da Ruga su manta da batun mulki – Tanko Yakasai

Tanko Yakasai
Tanko Yakasai

Fitaccen dan siyasar nan Alhaji Tanko Yakasai ya ce idan har ’yan kabilar Ibo ba su amince da batun samar wa makiyaya ruga a yankinsu ba, to su manta da batun yin mulkin Najeriya.

Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana haka ne lokacin da yake tattauanwa da Aminiya a Kano kan rashin goyon bayan da kabilar Ibo suka nuna game da shirin da Gwamnatin Tarayya ke yi na ganin an sama wa Fulani makiyaya killatattun wuraren kiwo a kokarinta na kawo karshen rigingimun makiyaya Fulani da manoma.

ADVERTISEMENT

Alhaji Tanko Yakasai ya ce idan har Ibo suka ci gaba da nuna rashin goyon bayansu ga dukkan abubuwan da ke ci gaba ne ga Arewa, to su ma ba za su samu goyon bayan Arewa ba a kokarinsu na ganin sun yi mulki a shekarar 2023. “Muna sane wannan fa ba shi ne karo na farko da Ibo suke sukar duk wasu shirye-shirye da Gwamnatin Tarayya take bullowa da su don ganin ta magance wannan rikici na makiyyaa da manoma ba. Ina ganin wannan shi ne shiri na uku amma suna nuna rashin goyon bayansu. Don haka lokaci ya yi da za su ajiye wannan akida tasu a gefe,” inji shi.

Alhaji Tanko Yakasai ya shawarci kabilar Ibo su rika goyon bayan sauran bangarorin kasar nan duk lokacin da za a yi musu wani abu na ci gaba, hakan zai sa sauran bangarorin su ma su goya musu baya a duk lokacin da za a kai wani abu na ci gaba yankinsu.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, “Tunda kowane bangare na kasar nan ya shugabanci kasar nan har da bangaren kananan kabilun kasar, ina ganin lokaci ya yi da ita ma kabilar Ibo za ta samu damar yin shugabanci musamman a shekarar 2023.”

Alhaji Tanko Yakasai ya yi kira ga al’ummar kasar nan cewa, “Duk lokacin da gwamnati ta bullo da wani shiri ko wata magana da take ganin mafita ce, idan mutane suka ga akwai gyara a ciki, to ba wai fitowa za su yi suna sukar abin ba. Kamata ya yi su lalubo wata hanyar da suke ganin ita ce mafita ko ita ce za ta magance waccan matsalar su kawo ta don a gwada a gani ko za ta yi aiki.”