Da Dumi Dumi

Idan Sanata Goje ya koma APC za mu janye shi daga majalisa – Yayari

Alhaji Ahmad YayariShugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Gombe Alhaji Ahmad Yayari, ya ce da zarar Sanatan yankinsu Alhaji Muhammad danjuma Goje, ya kuskura ya canja sheka daga Jam’iyyar PDP da aka zabe shi ya koma Jam’iyyar APC za su tura ya dawo domin ba su yake wakilta ba.
Alhaji Ahmad Yayari, ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a garin Kumo hedkwatar karamar Hukumar Akko a yayin da Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo, ya kai rangadi a ziyarar mazabun sanatoci uku da ya gudanar.
Alhaji Yayari, wanda ya yi kwamishina na tsawon shekara takwas a gwamnatin Goje ya ce su al’ummar Gombe ta Tsakiya musamman mutane garin Kumo ba su amfana da gwamnatin baya ba, domin duk girman garin Kumo babu aikin Naira miliyan goma a shekara takwas din da gwamnatin ta yi.
Ya ce ko hanyar mararabar Zambuk zuwa Lubo da Hinna zuwa Gwani a yankin Yamaltu Deba marasa inganci ne don haka ya kira yi Gwamna dankwambo ya sake su domin daidai suke da ba a yi ba.
Shugaban Ma’aikatan ya tabbatar wa Gwamana dankwambo cewa su mutanen Gombe ta Tsakiya Jam’iyyar PDP suke yi kuma ta Bamanga Tukur, Sanatansu Alhaji danjuma Goje, ya tashi a gaban duniya ya ce shi dan sabuwar PDP ne. “Yanzu haka muna jin rade-radin cewa zai koma Jam’iyyar APC idan ya koma ba mu yake wakilta ba don haka Gwamna ka sani daga ranar da muka ji ya koma APC mu al’ummar mazabar Gombe ta Tsakiya kamar yadda muka kai shi haka za mu dawo da shi,” inji Yayari.
Ya kara da cewa mutanen Gombe ta Tsakiya sun gaya masa cewa kada ya yi magana ya zuba ido kawai suna jira su ga wanda zai ba da gidansa ko ofis a kafa ofishin Jam’iyyar APC.
Shugaban Majalisar Jihar Gombe Alhaji Inuwa Garba, ya ce su mutanen yankin Yamaltu Deba da take yankin bakinsu daya da mutanen Akko ba sa wata sabuwar jam’iyya in ba PDP ba, inda ya ce ba su da zabi idan suna son ci gaba face su bi Gwamna dankwambo wajen sake ba shi dama ya yi Gwamna karo na biyu. Ya ce Gwamnan ya yi kokari an ba dansu Ministan Sufuri wanda kasafin kudin ma’aikatarsa ya fi na yankin Arewa maso Gabas.
Da yake maida jawabi Gwamna dankwambo ya nuna farin kan irin hadin kai da goyon baya da suka ba shi musamman lokacin da Shugaban kasa ya ziyarci jihar a lokacin taron tattalin arzikin kasa na shiyar Arewa maso Gabas.
Sai ya yi kira ga matasa su hada kai wajen neman abin yi don su dogara da kansu, kuma ya yi kiran su tashi su nemi Keke NAPEP da tasi-tasi da za a bayar don samun abin dogara da kansu.

Share