Da Dumi Dumi

Ighalo da Obi sun daina yi wa Eagles kwallo

Rahotannin da ke fitowa daga Masar sun nuna ’yan kwallon Super Eagles biyu John Mikel Obi da Odion Ighalo sun daina bugawa kasar haihuwarsu kwallo.

’Yan kwallon sun yi murabus ne jim kadan bayan Najeriya ta gama a matsayi na uku a Gasar Cin Kofin Afirka ta bana.

Yayin da Obi ya sanar da yin murabus a shafin sada zumuntarsa na Facebook a shekaranjiya Laraba, shi kuwa Ighalo tashar Brila FM da ke Abuja ce ta sanar da yin murabus dinsa a jiya Alhamis.

Mikel Obi yana da shekara 32 da haihuwa yayin da Ighalo yake da shekara 30 kuma dukkansu sun dade suna yi wa Eagles hidima kafin yin ritayar.

ADVERTISEMENT
Share