✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ilimin mata na da matukar muhimmanci ga al’umma – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya ce ilimin mata yana da matukar…

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya ce ilimin mata yana da matukar muhimmaci ga  al’umma.

Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen taron yaye daliban makarantar koyon kiwon lafiya, ta Sahlan da ke garin Jos karo na uku, da aka gudanar a ranar Asabar da ta gataba.

Ya ce ilimin mace yana da matukar muhimmanci a cikin al’umma, domin mace ita ce uwa da take rainon ’ya’ya. Ya ce don haka ya kamata a sanya ’ya’ya mata su karanci kowane fanni na ilimi, musamman ilimin kiwon lafiya.

“Na yi matukar farin cikin ganin irin yaranmu da wannan makaranta ta koyar da su kiwon lafiya ta yaye. Babu shakka idan aka ci gaba da yin irin wannan aiki, kasarmu za ta yi kyau nan gaba. Don haka mu ci gaba gaba da kafa irin wadannan makarantu, kuma mu ba su goyon baya,” inji shi.

Sheikh Jingir ya bayyana goyon bayansa ga matakin da gwamnati ta dauka na kawar da gidajen kangararrun da aka gina ba bisa ka’ida ba a kasar nan.

Ya ce ganin irin abubuwan da wadannan gidaje suke yi, ya dace gwamnati ta kawar da su, domin abubuwan da masu wadannan gidaje suke yi sun saba wa Musulunci da dokokin kasar nan.

Ya ce ya kamata gwamnati ta gina gidajen kangararru ta rika kula da su, ta samar musu da abinci da kwararrun masu karantarwa.

A jawabin Kwamishinan Sufuri na Jihar Filato Malam Muhammad Muhammad Abubakar ya bayyana cewa samar da irin wannan makaranta, wani babban abin alfahari ne ga al’umma. Don haka ya zama wajibi a taimaka wa wannan makaranta domin ta ci gaba da dorewa.

Ya ce idan aka samar da irin wadannan makaratu a wurare za a samu ma’aikatan kiwon lafiya, a dukkan asibitocin da ake da su a kasar nan.

Sai ya yi kira ga jama’a musamman masu hali su taimaka su gina irin wadannan makarantu.

A jawabin wani mai taimakon al’umma a garin Jos, Alhaji Abubakar Sadik Plaza cewa ya yi ilimin kiwon lafiya wani bangare ne da yake da matukar muhimmanci.

Ya yi kira ga iyaye su rika tura ’ya’yansu zuwa irin wadannan makarantu na kiwon lafiya, domin a samu isassun jami’an kiwon lafiya a kasar nan.

Tun farko a jawabin Shugaban Makarantar, Malam Muhammad Shafi’u Yakubu ya ce wannan yaye daliban shi ne karo na uku, a  makarantar.

Ya ce daga lokacin da suka bude makarantar zuwa yanzu, sun yaye dalibai maza da mata sama da 300 a fannonin kiwon lafiya daban-daban da suka hada da fannin ilimin jinya da ilimin gwaje-gwaje da ilimin bayanai kan kiwon lafiya.

“Baban burinmu shi ne mu ci gaba da bunkasa wannan makaranta ta hanyar kawo wasu fannonin kiwon lafiya. Kuma muna da burin ganin mun kai ga kafa jami’a a wannan gari na Jos,” inji shi.