Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Illolin yin talla ga ’yan mata  (1)

Illolin yin talla ga ’yan mata  (1)

Kusan ya zama ruwan dare ’yan mata su rika talla a birane da kauyukan kasar nan, musamman Arewa, duk da manazarta da dama na ganin wannan zamanin ya wuce. Ana maganar zamanin da ake shirin sarrafawa daga zaune, domin kullum duniyar dunkulewa take yi a waje daya.

Take hakkin ’ya mace ya wuce wai a lalata ta ko a yi mata fyade, domin sau da yawa ita ke kai kanta, kin ba ta damar cimma burinta shi ma take hakki ne. A kan haka ne wadansu kan yanke hukuncin cewa iyaye kan karfafa wa ’ya’yansu wajen zinace-zinace, da tu’amuli da miyagun kwayoyi da madigo, kai har hijira daga kasar, inda suke zama bakin haure, musamman idan mutum ya kalli yadda suke shiga ta yadda suke bayyana tsiraicinsu, har su rika yi maka tayi shin ba ka son abin da ka gani ne?

ADVERTISEMENT

Bayan cinikin, su rika kiranka da maigida, yaya ko baba suna rangwada suna karya murya don su sace maka zuciya. Wadansu jagororin haya ake dauko su, sannan jagora na da kusanci da jagaliya, alaka da almajira, kuma su ne a kasa da talakawa a al’umma.

Da farko iyaye mata kan koya wa yara talla, yayin da yaran suka gane irin ribar da ake samu sai su guje wa makaranta, domin wadansu da sun dawo sun wurgar da jakar littattafan sai gobe da safe! Sannan kai kanka ka san wadansu jagororin mabaratan nan da biyu suke jansu, wadansu ma hayarsu ake yi, sai su caba ado, a bi tituna ana karbar na yau, kafin gobe wadansu suna aje magana! Musamman a duniyar da wayar salula kan taka rawar gani wajen haduwar sirri da mahada.

ADVERTISEMENT

Wadansu iyayen kan nuna cewa da tallar yarinya za ta tara abin da za ka hada kayan daki, wai su ma tallar suka yi! Duk da cewa wadansu matasan kan samu horon kasuwanci daga tallar da suka yi lokacin kuruciya.

A haka wani zai samu jarin da zai kafa kansa har ya zama wani madugu.

Wani abin takaici da dama daga cikin masu tallar nan Musulmi ne, suna da iyaye ba marayu ba ne, abin tambaya a nan shin haka Musulunci ya umarce mu? Kuma kai me kake nema da har sai ’ya’yanka sun fita talla?

Wadansu daga safe har dare suna kan su kai karfe tara zuwa goma na dare kafin su nemi mai babur ya kai su kauyukansu! Ba boko ba Islamiyya, ana maganar karni na 21 inda ake tallar fura da nono ta kwanfuta, a yi ciniki da salula!

Wannan matsala ta talla ta haifar da matsaloli ga al’umma, kuma tana ci gaba da yada rashin kunya a tsakanin ’ya’ya da mahaifansu, sai kuma rashin ganin kimar malamai, dattijai da duk wani mai fada-a-ji a unguwa! Su ki karatu, sai gulma da kinibibi.

Irin wadannan matan da suke talla sun fi yiwuwar zama zaurawa, da dillalai ko kilakai masu zaman kansu. Tabbas ilimi na kara wa ’ya mace daraja da kima a kasuwar mata.

Za mu ci gaba

buharidaure@gmail.com

Modoji, Katsina.