✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina ma ’yan siyasa za su yi koyi da Dujiman Zazzau

Assalamu alaikum, ma’aikata da makaranta Jaridar Aminiya mai albarka. Ina muku gaisuwa da fatar alheri. A yau na shigo wannan fili ne domin in yi…

Assalamu alaikum, ma’aikata da makaranta Jaridar Aminiya mai albarka. Ina muku gaisuwa da fatar alheri.

A yau na shigo wannan fili ne domin in yi jinjina da taya murna ga Dujiman Zazzau na farko, Malam Sama’ila Suleiman, dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Dujiman Zazzau na farko  saboda nasarorin da yake samu a siyasance.

Wannan nadin ko shakka babu ya yi daidai kuma ya zo a daidai lokacin da ya kamata lura da yadda al’ummar Kaduna ta Arewa suke shan romon dimokuradiyya saboda wakilcin da yake yi musu cikin mutunci da kokarin ganin ci gabansu.

Babban nasarar da Sama’ila Suleiman ya samu da ya cancanci yabo da godiya shi ne yadda yake tafiya da matasa a harkokin siyasa, kasancewar shi ma matashi ne.

Ya kasance daya daga cikin matasan shugabannin kananan hukumomi lokacin da ya rike Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, kuma a wancan lokacin matasa sun gani a kasa, kuma dukkan mutanen karamar hukumar sun gani a kasa. Kuma har ya kammala wa’adinsa ya sauka, kowa na sam barka.

Da a ce sauran ’yan majalisa da sanatoci da sauran masu rike da mukaman siyasa za su yi koyi da yadda Sama’ila Suleiman ke tafiya da matasa da taimakonsu, da Najeriya ta zauna lafiya domin dama matasa su ne kashin bayan ci gaba kowace al’umma. Idan matasa suka samu sana’o’in da za su rike kansu, suka fara rike madafun iko, komai zai dawo yadda ya kamata.

Amma irin yadda wadansu ’yan siyasa suke yin watsi da matasa, su mayar da su saniyar ware wajen gudanar da harkokin mulki, ba za a nemo su ba sai lokacin da siyasa ta zagayo, wannan ba karamar matsala ba ce ga ci gaba kasar nan da kuma kara jefa kasar cikin jahilci da matsaloli.

Amma a siyasa irin ta Dujiman Zazzau, yakan ce wa matasa su dage da karatu da sana’a domin su ne shugabannin gobe. Kuma bai yi kasa a gwiwa ba, domin tuni ya fara tsayawa kai da fata ya ga matasa sun fara tsayawa takara domin su zauna da kafafunsu. Sannan ya samar ma wadansu da sana’o’in hannu, ya tura wasu makaranta su karo ilimi, sannan ya jawo wadansu kusa da shi su san makaman aikin siyasa.

Ina kira ga manyan ’yan siyasa da su sani cewa kusan duk ’yan siyasa koya suke yi, ko kuma koyar da su ake yi. Idan ba a koyar da matasa ba, aka jawo su jiki, su waye za su zama shugabannin gobe?

Daga Malam Muhammad Kabir Zuruboy Kawo, Kaduna

08069118686