✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina nan da raina – Baba Ari

A ranar Asabar da ta gabata ne aka baza labarin mutuwar dan wasan barkwanci Sani Adamu Ari, wanda aka fi sani da Baba Ari.A labarin…

A ranar Asabar da ta gabata ne aka baza labarin mutuwar dan wasan barkwanci Sani Adamu Ari, wanda aka fi sani da Baba Ari.
A labarin an ce jarumin ya mutu ne a ranar Juma’a ba tare da an bayyana musabbabin mutuwarsa ba.
Wakilinmu ya tuntubi dan wasan inda ya karyata jita-jitar. Ya ce: “Babu abin da ya same ni, asali ma ko ciwon kai ban yi ba. Kuma idan ajali ya yi kira mutum ba zai kara ko sakan daya ba.”
A karshe ya nemi jama’a su guji yada jita-jita.