✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina Za Mu A Nes Lebul? (2)

Za a tsokano wannan yanayi ne domin mu fahimci dalilan da suke sa wadansu gungun jama’a ke amfani da karfin tuwo a wajen gudanar da…

Za a tsokano wannan yanayi ne domin mu fahimci dalilan da suke sa wadansu gungun jama’a ke amfani da karfin tuwo a wajen gudanar da mulki a mimakon lalama da ban magana. Yin haka zai taimaka wajen zayyana hoton rayuwar dangantakar da ke tsakanin gwamnati da wadanda take mulka da kuma fiddo fili damar da jama’a ke da ita ta mika kai ko kuma bijirewa a cikin irin wannan tsari.

Za mu fara dubin tsarin ne tun daga zamanin mulkin mallaka domin tattauna rawar da En’e-En’e da ’yan doka da alkalai suka taka wajen haifar da tsarin tashin-tashina da rashin daidaiton tunani a siyasance da kuma dangantakar da ke tsakanin jam’iyyun siyasa a cikin irin wannan badakala.

Domin ganin yanayin tsarin sosai za mu yi kokarin amsa tambayoyi da suka hada da wace irin rawa hukumomin En’e-En’e suka taka wajen inganta ko kuma lalata juriyar jama’a ta son yin awon gaba da mulkin danniya? Wace rawa sarakuna da hakimai da dagatai da masu unguwa suka tako a wannan badakala? Wace irin dangantaka ce tsakanin jam’iyyun a bangare guda da kuma sarakuna da masu mulkin mallaka da sauran jama’a a wani bangaren? Wane irin tasiri wannan dangantaka ta yi wajen aza tubalin gwagwarmaya da harsashin ginin kasa, musamman a tsarin mulkin danniya da kuma wariya? Za a amsa wadannan tambayoyi ne domin fuskantar yadda wannan tsari na wariya da danniya ta hadin gwiwar sarakunan gargajiya da ’yan mulkin mallaka ya samar da rashin jituwa da daidaito a tunanin mutanen Najeriya, musamman daga Arewacin kasar.

Zangon siyasa na farko a Najeriya, duk da cewa ba abin alfahari da murna ba ne ga wasu, ganin cewa zango ne da yawancin ’yan adawa ba su ji dadin rayuwa ba, amma wannan a maimakon ya sa jama’a su saduda, sai ma ya kara sa musu karsashi da ba su damar amfani da mabambantan dabashiri don yakar gwamnatin danniya da mulkin murdiya da kisan mummuke.

A duk lokacin da ake son a fahimci yanayin dunniya da babakera da kuma tashin-tashina a cikin al’umma ya kamata a kalli matsalar ta fuskar su wane ne ake dannewa, su wa ke danniyar, kuma me ya sa ake yin danniyar daga karshe a nemi sanin wace manufa ake son cimma? Ba za a ga amsar wadannan tambayoyi a fili ba sai an yi nazarin dangantakar da ke tsakanin al’ummu da yadda ake gudanar da tattalin arzikin al’umma bisa irin tsarin da ta ginu, musamman irin zaman kaskar da ke gudana tsakanin wadanda ake tatsa da irin tsarin da aka dasa domin tatsar tasu. Dangane da haka irin zaman tuwo da miya da ke tsakanin “tsarin tattalin arziki” da “tsarin mulki” a yawancin lokutta shi ke haifar da tsarin zaman danniya da cin zali, ya kuma sa tsarin kaskanci ya ci gaba da tabbata.

Idan aka dubi irin wannan tsari a kasashen da suka ci gaba ta jari-hujja za a ga cewa ita dukiya a wurin su, mallakar mai ita ce, gwamnati na sa baki ne kurum a cikin harkar gudanar da wannan dukiya wajen tabbatar da gudanuwar dukiya ta hanyar doka da inganta ko kyautata hanyoyin cin riba (ko kuma riba) da samar da haraji ko kudin shiga. Duk da cewa kasashe masu tasowa sun antaya cikin tsarin jari-hujja na duniya, sun yi haka ne ba tare da son su ba, wanda ya sa dole ake ganin burbushin tsarin mulki na gargajiya da kasashen suka gada can da tare da su. Da wannan tsarin danniya na gargajiya ne ’yan mulkin mallaka suka ci gaba da tatse da kuma tsotse arzikin al’ummu masu tasowa duk da cewa sun shiga da nasu tsarin na zamananci.

A Arewacin Najeriya, gargajiya ta saje ne da zamananci, masu mulki na gargajiya su ne suka daura aure da ’yan mulkin mallaka ta hanyoyi daban-daban, kuma ta haka suka amfana da juna. ’Yan mulkin mallaka sun tabbatar da samuwar tsarin mulkin En’e-En’e, suka yi wa tsarin shari’a kwaskwarima ya dace da tsarin mallaka, aka shigo da sababbin hanyoyin karbar haraji, Turawan mulkin mallaka suka baje kolinsu, suka ci karensu ba babbaka, kodayake a wadansu wurare kafin su kai wuka ga karnukan, sai da karnukan suka yi musu haushi, wasu ma da yakushi, duk da cewa an babbake su daga baya.

An kawo wannan dogon bayani ne domin mu fahimci cewa tashin-tashina da fafutukar samar da ’yancin kai a cikin kasa ba abu ne da kawai ake samu a gargajiyance ba, har da a zamanance. Tashin – tashina ba wai ta tsaya ga amfani da karfin towo da ba hammata-iska a tsakanin mabambanta ra’ayoyi ba kurum, ko kuma tayar da kayar baya da ihuce-ihuce a fagen siyasa ba. Wannan ya sa aka rarraba tashin-tashinar zuwa ta kusa da ta nesa. Tashin-tashina ta kusa ba ta wuce wadda ke kai ga bugun mutum ba da bata masa rai, wadda kuma doka ba ta amince da ita ba. Sai dai wannan kashi, bai tsaya ga jin ciwo kadai ba, har da niyyar aikata haka din, musamman idan ta tayar da hankalin wani ko wasu. Kodayake a nan ana maganar doka da tsari, sai dai ba mai iya cewa ga tashin-tashina da ke bisa doka ko kuma ga wadda ta saba ka’ida, ko kuma a ce ga inda ta ka’ida ta tsaya ga inda wadda ba ta ka’ida ba ta soma.

Wannan shi ya sa ake ganin cewa ya dace a sake dubar ma’anar tashin-tashina da tunanin jibga duk wani abu da ya zame kandagarki wajen ciyar da dan Adam gaba; ke nan wadda ake yi wa mata kurum, akwai ta wariyar launin fata, akwai ta tsakanin ma’aurata, akwai tsakanin kabilu da addini da ta masu shan kwaya da kuma ta yau da kullum:- kamar latsa odar mota da karfi da fashewar taya ko gara gara gare a cikin unguwa da ma  ta ihun jin dadi da wani ya yi. A takaice za a iya cewa, tashin-tashina ba ta wuce duk wani hani ko matsi da ake yi wa dan Adam ta fuskar take masa ’yancinsa ko shige masa cikin rayuwa ba.

Za Mu ci Gaba