✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IPOB ta debo ruwan dafa kanta —DSS

Hukumar tsaro ta DSS ta sha alwashin kamo ‘yan kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da suka kashe jami’anta a jihar Inugu.— Kakakin DSS, Peter…

Hukumar tsaro ta DSS ta sha alwashin kamo ‘yan kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da suka kashe jami’anta a jihar Inugu.—

Kakakin DSS, Peter Afunanya, ya bayyana hakan a takardar ta’aziyar hukumar ga dagi da iyalan jami’an a ranar Lahadi.

Afunanya ya ce, ‘yan IPOB sun afka wa jami’an ne a garin Emene da ke Inugu, a  lokacin da suke gudanar da sintiri.

“Hukumar ta rasa jami’ai biyu a harin da kungiyar IPOB ta kai musu ba tare da sun taba kowa ba.

“Saboda haka, Hukumar na mika ta’aziya ga iyalan jami’an da aka rasa, kuma muna rokon Allah Ya jikansu.

“Hakan kuma, mun dauki matakan da suka kamata domin tabbatar da mun kamo wadanda suka kashe su, da duk masu hannu a kisan, a kuma yanke musu hukunci”, inji shi

Ya ce za su gudanar da cikakken bincike kan abin da ya faru, tare da hadin kan sauran jami’an tsaro don tabbatar da tsaro ga al’umma.

Afunanya ya kuma bukaci mutanen gari da su cigaba da gudanar al’ammuransu na yau da kullum ba tare da fargaba ba.