✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta yi bikin Ranar Juyin Juya-Hali daidai lokacin da tankiya ta yi zafi tsakaninta da Amurka

Dubban Iraniyawa ne suka kwarara kan titunan birnin Tehran da sauran biranen kasar domin tuna zagayowar ranar juyin juya-halin Musulunci karo na 41, kuma hakan…

Dubban Iraniyawa ne suka kwarara kan titunan birnin Tehran da sauran biranen kasar domin tuna zagayowar ranar juyin juya-halin Musulunci karo na 41, kuma hakan na zuwa ne a daidai lokacin da tankiya ke karuwa a tsakanin kasar da Amurka.

Duk da tsananin  sanyin da ake yi, Iraniyawan sun yi fitar dango a ranar Talata zuwa Dandalin Azadi da ke birnin Tehran, suna daga tutocin kasar tare da rike hotunan wanda ya kirkiro Jamhuriyar Musuluncin marigayi Ayatollah Ruhollah Khomeini.

“Mutuwa ga Amurka” da “Za mu ci gaba da bijirewa har gaci” ne kalaman da ke rubuce a allunan da mahalarta taron suke rike da su.

Da yake magana a wajen gangamin, Shugaban Iran, Hassan Rouhani ya ce Amurka ta kasa samun “natsuwa” game da yadda juyin juya-halin Musuluncin ya ci gaba da wanzuwa a kasar na tsawon shekara 41, bayan kawar da gwamnatin dan koren Amurka, Sarki Shah.

“Abu ne da Amurka ba za ta iya samun natsuwa game da shi ba, kuma ta amince da nasarar da babbar kasa ta samu; kuma an ma fatattake ta daga cikin kasar nan,” inji Rouhani.

“Lallai ne a kansu (Amurka) cikin shekara 41 da suka gabata, suna ta mafarkin watan wata rana su sake sanya kafarsu a cikin kasar nan, sakamakon kwana da sanin cewa muna daga cikin manyan kasashe masu fada-a-ji a Gabas ta Tsakiya,” inji shi.

Ana gudanar da bukukuwan ne domin tuna ranar da jagoran mabiya Shi’a Khomeini ya koma kasar daga gudun hijirar da yake yi a waje inda ya hambare gwamnatin Sarki Shah.

Gwamnatin kasar ta yi kira ga al’ummar kasar su yi fitar dango domin nuna goyon baya ga gwamnatin, bayan da Iran din ta girgiza ainun daga manyan zanga-zangar adawa da hukumomin kasar da kuma tankiyarta da Amurka.