✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyaye da daliban makarantar Dapchi sun yi wa Leah addu’a

A yayin da daliba Leah Sharibu ta cika shekara guda a hannun ’yan Boko Haram bayan da suka dauke ta daga Makarantar Sakandaren ’Yan mata…

A yayin da daliba Leah Sharibu ta cika shekara guda a hannun ’yan Boko Haram bayan da suka dauke ta daga Makarantar Sakandaren ’Yan mata ta garin Dapchi a Jihar Yobe, a ranar Talata da ta gabata iyayen yara da daliban makarantar sun gudanar da taro inda suka yi  addu’o’i na musamman domin rokon Allah Ya sa a sako ta.

A gidan su Leah da ke garin Dapchi kuwa, mabiya addinin Kirista da na Musulunci ne suka gudanar da irin wadannan addu’o’i, suka roki Allah Ya kubutar da ita daga hannun wadanda ke tsare da ita tsawon shekara guda.

Mahaifiyar Leah, wacce take zaune da mijinta a Jihar Adamawa ta ce za ta ci gaba da zama a can har sai ’yarta ta dawo. Ta roki Gwamnatin Tarayya ta cika alkawarinta na tabbatar da cewa ’yarta ta samu ’yanci ta kubuta daga hannun wadanda suke garkuwa da ita.

Yayar Leah mai suna Hyelakumi Manasseh, wacce ta wakilci mahaifiyarta a wajen taron addu’ar da aka gudanar a Dapchi ta nemi Shugaba Buhari da ya mai da hankali wajen yin yarjejeniya da masu rike da ’yar uwarta domin ganin an sako ta da gaggawa.

“Mun shiga matsananciyar damuwa tun daga lokacin da aka kama Leah aka yi garkuwa da ita. Mun yi amanna cewa da ’yar Shugaban Kasa ce aka kama, zuwa yanzu da tuni an kwato ta koda kuwa nawa ne suka nema a biya su,” ta fadi haka cikin hawaye.

Sakataren Kungiyar Iyayen Yara na makarantar, Kachalla Bukar ya ce sun shirya gudanar da azumi da addu’o’in na musamman ne da nufin neman taimakon Allah, domin kuma su sanar da dukan duniya cewa fa har yanzu Leah tana tsare wajen masu garkuwa da ita.

Ni na bude wa Onnoghen asusun banki da Dala dubu 30 – Babban Lauya