✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyaye ku ba ilimin ’ya’yanku fifiko – Malam Namadi

Babban Limamin Masallacin Kungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah rashen Sabo, Abeokuta, Malam Muhammadu Namadi ya yi kira ga iyaye su bai wa ilimin…

Babban Limamin Masallacin Kungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah rashen Sabo, Abeokuta, Malam Muhammadu Namadi ya yi kira ga iyaye su bai wa ilimin ’ya’yansu fifiko domin shi ne abin da in suka bai wa ’ya’yan ba za su yi nadama ba a rayuwarsu.

Malam Muhammadu Namadi, ya ce akwai bukatar iyaye su bai wa ’ya’yansu ilimin addini domin rayuwarsu ta duniya da Lahira sannan su ba su ilimin boko domin zamantakewarsu ta duniya wanda shi ma za su yi amfani da shi ta hanyar da ya dace su samu babban rabo a ranar gobe Kiyama.

“Ilimin addini da na boko idan ka bai wa ’ya’yanka tamkar ka ba su fika-fikai biyu ne sai su yi amfani da su su tashi su je duk inda suke so su sauka lafiya. Amma idan yaro ya yi guda bai yi guda ba, za a samu nakasu don haka ya kamata iyaye su dage wajen bai wa ’ya’yansu ilimi domin shi ke kai mutum kololuwar matsayi da mukami,” inji shi.

Malam Muhammadu Namadi, ya bayyana haka ne a lokacin taron saukar karatun Alkur’ani na daliban makarantar Tarbiyyatul Islamiyya da ke Sabo Abeokuta da ya gudana a karshen makon jiya.

Shugaban Makarantar kuma jagoran Kungiyar Izala a garin Abeokuta Malam Ali Muhammad, kira ya yi ga iyayen yara su rika kokarin fitar da hakkin malaman makaranta da ke kula da tarbiyyar ’ya’yansu. Ya ce sau tari wadansu iyayen na kashe makudan kudi kan ilimin boko na ’ya’yansu amma ba sa iya biyan kudin wata na makarantun Islamiyya, “Wannan ne babban kalubalen da muke fuskanta wajen gudanar da wannan makaranta da ke bai wa ’ya’yanmu tarbiyya, wacce a wata mukan kashe Naira dubu 100 wajen biyan hakkoki da albashin malaman makaranta, sai dai sau tari abin da muke samu daga iyaye na kudin wata baya kaiwa Naira dubu 60. Wannan ya sa a lokuta da dama sai mun nemi taimako kafin mu iya biya hakkin malamai masu karantarwa. Da iyayen yara za su bada goyon baya su rika biyan kudin makarantar ’ya’yansu da ba sai an kai ga neman taimako ba kafin a biya malaman hakkinsu,” in ji shi.

Malam Ali ya ce Naira 500 suke karba a kan kowane yaro duk wata wadanda ba kudi ne na a zo a gani ba, idan aka kwatanta da abin da iyaye ke kashe wa ’ya’yansu a makarantun boko. Don haka akwai bukatar iyaye su rika fitar da hakkin malaman da ke koya wa ’ya’yansu addini.

“Wannan saukar karatun Alkur’ani na yara 23, ita ce karo na uku da makarantar ta yi a garin Sabo, Abeokuta, domin a farko mun taba yin saukar karatun matan aure ta farko, sannan shekara biyu da suka gabata mun yi ta dalibai yara ’yan makaranta sannan yanzu mun sake yin wannan. Abin da nake so in shaida wa iyayen yara da yaran kansu shi ne karatun masu saukar ba zai tsaya a nan ba, domin akwai karatun littattafan addini da sauransu don haka za mu sanya su a makarantun Islamiyya na gaba da wacce suka kammala domin ci gaban karatunsu. Fatarmu su yi aiki da ilimin da suka samu kuma iyaye su ci gaba da kula da tarbiyyarsu,” inji shi.

Dalibai 23 da suka yi sauka a makarantar Tarbiyyatul Islamiya da ke Sabo Abeokuta sun hada da maza 15 da mata 8, wadanda aka bai wa takardun shaidar kammala karatun Islamiyya matakin firamare. Kuma daliban da suka nuna kwazo sun samu kyaututtuka na musamman domin ba su kwarin gwiwa da kuma kara wa na bayansu kwazo da himma.

Malam Ibrahim Makinta, daya ne daga cikin iyayen daliban da suka yi saukar ya bayyana farin cikinsa inda ya yi kira ga iyaye su yi kokarin kula da tarbiyyar ’ya’yansu tare da ba su ilimi.

“Shekara biyu da suka gabata babban dana ya yi sauka a wannan makaranta sannan a bana ma an yi walimar saukar da ’yata ta biyu, wannan abin farin ciki ne a gare ni. Fatarmu iyaye mu dage da bai wa ’ya’yanmu tarbiyya, mu kuma ba su ilimin addini da na zamani,” inji shi.

Iyayen da sauran al’ummar garin Sabo Abeokuta sun yaba matuka lura da yadda Makarantar Tarbiyatul Isalamiyya ke bai wa ’ya’yansu tarbiyya.